Matashi ya mutu a gasar shan giya don hanƙoron lashe kyautan N198,000

Matashi ya mutu a gasar shan giya don hanƙoron lashe kyautan N198,000

Wani matashi mai shekaru 23 ya garzaya barzahu jim kadan bayan ya daddagi kwalban giya a gasar shan giya giyan daya gudana a wani gidan cashewa.

Matashi ya mutu a gasar shan giya don hanƙoron lashe kyautan N198,000
Matashi ya mutu a gasar shan giya don hanƙoron lashe kyautan N198,000

Matashin mai suna Kelvin Rafael sanannen mashayin giya ne, inda rahotanni sun bayyana cewar ya isa teburin abokansa ne inda ya tarar dasu sun sa kayautan N198,000 ga duk wanda ya shanye wata giya mai suna Tequila, nan da nan ya shiga gasar.

KU KARANTA: Osinbajo ya sake kai ziyara jihar Kaduna, ya tarbi wani shugaban ƙasa

Kafin kace kule, jama’a sun cincirindo akan su, suna kallo, shi kuwa Rafael ya dauki kwalbar giya Tequila ya dinga sha, yan kallo kuwa suna tayi masa kirari, nan dai ya riga kowa kammala shan nasa giyan ba tare da ya bar ko digo a kwalbar ba, jama’a nata mamakinsa, nan take aka bashi kyautansa na N198,000.

Matashi ya mutu a gasar shan giya don hanƙoron lashe kyautan N198,000
Matashi ya mutu a gasar shan giya don hanƙoron lashe kyautan N198,000

Sai dai ba’a nan gizo ke sakar ba, don kuwa jim kadan bayan Rafael ya amshe kudinsa, sai ya fadi sumamme, ya fita hayyacinsa, ko kafin a garzaya dashi asibiti, yace ga garinku nan! da aka isa da shi asibiti, Likitoci sun bayyana cewar Rafael ya mutu ne sakamakon giya.

Da wannan ake jan hankalin mashaya giya da cewa, yawan shan giya na da illa sosai ga laifyar dan adam.

Ga bidiyon a nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel