Fada ya barke yayinda wani mutumi ya sanya wa Karen sa suna Muhammad a Kaduna

Fada ya barke yayinda wani mutumi ya sanya wa Karen sa suna Muhammad a Kaduna

- Fada ya kaure a wani kasuwa dake jihar Kaduna lokacin da wani mutumin kabilar Igbo ya sanya ma karensa suna Muhammad

- A cewar rahotanni ya maida martani ne ga makwabcin sa wanda ya sanya ma karensa sunan sa

- Yan sanda sun shiga maganar don kawo karshen rikicin

Fada ya barke yayinda wani mutumi ya sanya wa Karen sa suna Buhari a Kaduna
Hoton kasuwar Panteka

Wani gagarumin fada ya barke a kasuwar sabon Panteka dake hanyar babban titin Nnamdi Azikiwe lokacin da wani mutumi dan kabilar Igbo ya sanya ma karensa suna Muhammad.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa jami’an hukumar sojin Najeriya da suka mamaye yankin don dawo da zaman lafiya da doka bayan barkewar fadan sun rufe kasuwar.

Kasuwar Panteka ta kasance matatarar masu gyaran ababen hawa a jihar, wanda ke dauke da garejin bakanikai da yawa.

KU KARANTA KUMA: Sojojin Najeriya da Kamaru sunyi gagarumin aiki a yankin iyakar kasashen biyu

Wani shaidan gani da ido Aminu Ibrahin ya ce rikicin ya fara ne lokacin da wani Muhammad ya siya kare sannan ya sanya ma Karen sunan wani mutumin Igbo mai siye da siyarwa.

“Tunda yaron ya sanya ma Karen sunan dan kasuwar, dan kasuwar na ta gargadin shi lokuta da dama kan cewa ya canja ma Karen suna, amma mammalakin Karen Muhammad ya ki. Wannan yasa shima Ibere ya siya kare sannan ya sanya masa suna Muhammad, a lokacin ne rikicin ya barke sosai,” cewar shaidan na gani da ido.

Yace sai fada ya daure tsakanin yan kasuwa Hausawa da Inyamurai a kasuwar wanda ya kai har saida yan sanda suka rufe kasuwar.

Ba’a samu daman jin bayani daga bakin kakakin yan sanda ba a lokacin da ake kawo wannan rahoton kamar yadda bai amsa kiran wayarsa ba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel