Kalli abinda aka kama gwamna Fayose yana yi a shagon wata mata

Kalli abinda aka kama gwamna Fayose yana yi a shagon wata mata

A daidai lokacin da ake bikin zagayowar ranar mata ta duniya, kwatsam sai aka tsinci gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose yana dinki a keken taka taka.

Kalli abinda aka kama gwamna Fayose yana yi a shagon wata mata
Kalli abinda aka kama gwamna Fayose yana yi a shagon wata mata

A jiya Talata 7 ga watan Maris ne aka hangi gwamnan a shagon wata mata cikin kasuwar Ado Ekiti yana dinka atamfar da zai sanya a ranar murnan zagayowar ranar mata ta duniya, wato yau Laraba 8 ga watan Maris kenan.

KU KARANTA: An rage ma Malamai 11 muƙami a jihar Kros Ribas, sun koma masu gadi

Tsabagen shirya ma bikin ranar matan, har hutun aiki gwamnan ya baiwa dukkanin ma’aikatan jihar.

Kalli abinda aka kama gwamna Fayose yana yi a shagon wata mata
Kalli abinda aka kama gwamna Fayose yana yi a shagon wata mata

Kamfanin dillancin labarai, NAN, ta ruwaito cewa gwamnan ya bada hutun ne don maza ma su shiga cikin bikin ranar matan a dama dasu ba yadda ya kamata. Gwamna Fayose yace gwamnatinsa zata dauki nauyin hidiman bikin don baiwa mata daman nuna basirarsu, tare da nuna musu ana tare.

Sama da mata 45,000 ne daga kowane bangaren aiki da kasuwanni suka nuna sha’awarsu na shiga hidimar bikin ranar mata ta duniya da za’a yi a babban birnin jihar Ekiti, Ado Ekiti. Sa’annan gwamnan ya siyar musu da turmin atamfa na N3,500 akan naira 500 a matsayin tallafinsa don saukaka musu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel