Masu jirage, yan kabu kabu za su yi rashi domin rufewan filin jirgin sama na Abuja

Masu jirage, yan kabu kabu za su yi rashi domin rufewan filin jirgin sama na Abuja

- Idan aka dauki jirgin da mutane ba su cika shi ba, ya zama fadowa kuma abin da zai rika faru kenan kwanan nan

- Rufewan filin zai dame su ta hanyar samun biyan bukatan su

- Masu mota kuma sun nuna rashin jin dadi mataki gwamnatin akan yadda za su rufe filin jirgin

- Yawanci direbobin za su rasa aiki acikin sati 6 domin kalilan su ne za su je Kaduna

Masu jirage, yan kabu kabu za su yi rashi domin rufewan filin jirgin sama na Abuja
Masu jirage, yan kabu kabu za su yi rashi domin rufewan filin jirgin sama na Abuja

Yawanci yan aiki jiragen sama da masu kabu kabu na daukan mutane a filin jirgin sama na Abuja, sun fara kuka akan yadda rufewan filin zai dame su ta hanyar samun biyan bukatan su.

Abdullahi Saroke, maneja kamfanin tashi da saukar jirgi, Azman ya fada cewar, kashi 65 na tafiya akan jirgin sama ne zaa yanke daga filin jirgin Abuja. Ya ce wannan fadowa ne gare sun da su ke aiki jirgi a Kaduna. Ya ce idan aka dauki jirgin da mutane ba su cika shi ba, ya zama fadowa kuma abin da zai rika faru kenan kwanan nan.

KU KARANTA: Bankuna 3 zasu kwace kamfanin Etisalat a yau akan bashin N541.8 billion

Yadda ake ciki yanzu, yawan mutane da suke tafiya da jirgin sama za su fara tafiya da mota. Ya ce: “Abin da na gani shi ne, za mu rika tafiya Kaduna ama ba duka hanya za rika bi ba. “Idan aka cigaba aka nan, yawanci kamfani za su rufe.

“Kashi 65 na tafiya tsakanin Abuja da Legas za rufe tun daga kwana 8 na watan Maris.

“Wannan ya nuna cewar, kashi 65 aka yanka sai ya rage kashi 35 da zai rika aiki kuma su 65 suka fi kawo mana kudi."

KU KARANTA: An kuma dawo da ‘yan Najeriya 171 daga kasar Libiya

Ya ba gwamnati shawara cewar, idan mutane basu samu tafiya ba, ba masu kamfanoni ne suke da laifi ba, tun da gwaminati ne ya ke rike da lokacin da za samu tafiya. "Ba mu ne za mu sa su a gidan hutu ba idan ya faru aka nan, ” ya ce.

Masu mota kuma sun nuna rashin jin dadi mataki gwamnatin akan yadda za su rufe filin jirgin. Mallam Aliyu Abdullazeez-Aliyu, Ciyaman na kungiyar yan direba na Abuja ya ce mutane shi za su rasa wajen milyan N300 domin rufewan.

Yawanci direbobin za su rasa aiki acikin sati 6 domin kalilan su ne za su je Kaduna. Ya ce za su tura mutane 150 ko 200 zuwa Kaduna aiki ne kawai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel