Gaba-da-gabanta: Majalisar wakilai zata binciki hukumar EFCC

Gaba-da-gabanta: Majalisar wakilai zata binciki hukumar EFCC

Majalisar wakilai karkashin jagorancin Yakubu Dogara tace zata fara binciken ayyukan hukumar nan mai yaki da cin hanci da rashawa watau EFCC don duba yadda take ayyukan ta.

Gaba-da-gabanta: Majalisar wakilai zata binciki hukumar EFCC
Gaba-da-gabanta: Majalisar wakilai zata binciki hukumar EFCC

Majalisar ta dauki wannan matakin ne bayan da suka gama muhawara a kan wani kuduri da dan majalisa Babajimi Benson daga jihar Legas ya kawo yana bukatar majalisar ta yi bincike kan yadda EFCC ke kwatar kayan mutane da kadarori tare da kudu sannan kuma a ina take kai su.

Majalisar ta koka a kan yadda tace kadarorin da aka kwata ana barin su ne a banzace inda wani lokaci ma har sukan fara lalacea wanda kuma ba haka ya kamata ba.

KU KARANTA: Yan shi'a basu da bambanci da yan ta'adda

A wani labarin, Tsohon manajan rukunin kamfanonin mai na Najeriya watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC), Andrew Yakubu ya shigar da kara yana tuhumar EFCC da gwamnatin tarayya.

Andrew Yakubu ya maka EFCC din ne tare da gwamnatin tarayya inda yake kalubalantar sama shin da sukayi tare da abun da ya kira kwace mashi kudin sa a garin Kaduna.

A karar da ya shigar a gaban babbar kotun tarayya dake a garin Abuja, Lauyan da ke kare shi Ahmed Raji (SAN) ya shaidawa kotun cewa suna bukatar kotun ta tilastwa EFCC da gwamnatin tarayya su ba wanda yake karewa N1biliyan domin sun tozarta shi sannan kuma su fito cikin jarida su bashi hakuri.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel