Daga karshe, Makarfi, Fayose sun dau na annabawa, sun amince da Modu Sherrif a matsayin shugaban PDP

Daga karshe, Makarfi, Fayose sun dau na annabawa, sun amince da Modu Sherrif a matsayin shugaban PDP

- Daga karshe, gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose da Sanata Makarfi sun amince da Ali Modu Sherrif a matsayin shugaban jam’iyyar PDP

- Shugaban kwamitin sulhu, Gwamna Seriake Dickson na jihar Bayelsa yace siyasa ne kawai zata dawo da zaman lafiya jam’iyyar PDP

- Bangaren Makarfi sun amince da Modu-Sherrif kuma shine zai shugabanci jam’iyyar a taron gangamin da za’ayi a 30 ga watan Yuni

Daga karshe, Makarfi, Fayose sun dau na annabawa, sun amince da Modu Sherrif a matsayin shugaban PDP
Daga karshe, Makarfi, Fayose sun dau na annabawa, sun amince da Modu Sherrif a matsayin shugaban PDP

Rikicin shugabancin da ke damun babbar jam’ iyyar adawa ta PDP tazo karshe bayan bangaren Ahmed Makarfi sun amince da Ali Modu Sherrif a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

Wannan abu ya faru ne a ranan Talata, 7 ga watan Maris, yayinda kwamitin sulhu ta sallama rahoton ta karkashin jagorancin Gwamna Seriake Dickson a sakatariyan jam’iyyar da ke Abuja.

KU KARANTA: Kasar Italiya ta bankado yan Najeriya 37

Jaridar PM news ta bada rahoton cewa Makarfi ya amince da cewa Modu-Sherrif ya jagoranci taron gangamin jam’iyyar da za’a gudanar a ranan 30 ga watan Yuni.

Yayinda yake Magana da manema labarai bayan sallama rahoton, gwamna Dickson yace sulhu ta hanyar siyasa shine hanye mafi kwarai, cigaba da zuwa kotu kawai zai kara raba kan yan jam’iyyar PDP.

Yace:“Idan aka ce kotun afil ko kotun koli, dole ne zamu gudanar da taron gangamin, saboda haka sulhun siyasa yafi.”

Dickson ya bayyana cewa suna sa ran taron gangamin ta taimaka wajen kawo cigaban jam’iyyar.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel