Mukaddashin shugaban kasa ya cika 60 a Duniya

Mukaddashin shugaban kasa ya cika 60 a Duniya

Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya cika shekaru 60 a Duniya da haihuwa a yau Laraba 8 ga watan Maris. Muna taya shugaban kasa na rikon kwarya murnar zagayowar ranar haihuwar sa.

Mukaddashin shugaban kasa ya cika 60 a Duniya
Mukaddashin shugaban kasa ya cika 60 a Duniya

A yau ne Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo yake cika shekaru 60 a Duniya. Osinbajo dai ke rike da Najeriya tun bayan tafiyar shugaba Buhari a tsakiyar watan Junairu. Jama’a na ta kara yabawa Farfesan inda suka ce bai ba da kunya ba.

Osinbajo ya tashi tsaye wajen harkar gyara tattalin arzikin kasar da kuma sawwake harkar kasuwanci. A jiya ne ma dai aka kaddamar da aikin jirgin kasan Legas da gwamnatin Buhari tayi alkawari. Mukaddashin ya kuma kewaya Yankin Neja-Delta domin kawu karshen rikicin yankin.

KU KARANTA: Osinbajo ya rantsar da sabon Alkalin Alkalai

Mukaddashin shugaban kasa ya cika 60 a Duniya
Mukaddashin shugaban kasa ya cika 60 a Duniya

Kwanan nan shugaban kasar na rikon-kwarya ya bayyana yadda wannan gwamnati za tayi kokari wajen kawo karshen cin hanci da rashawa a Najeriya. Osinbajo yace za a bi irin matakan da suka bi lokacin yana Kwamishinan shari’a a Jihar Legas.

Kakakin Majalisa Rt. Hon. Yakubu Dogara ya taya Osinbajo murnar wannan rana inda yace tabbas Osinbajo ya nunawa kasa da Duniya cewa ya san me yake yi. Kwanaki aka nadawa Farfesa Yemi Osinbajo Sarautar ‘Obong Emem’ na Garin Akwa Ibom.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel