Mutanen arewa ba zasu taba yarda dan kabilan Igbo ya shugabanci Najeriya ba - Uwazuruike

Mutanen arewa ba zasu taba yarda dan kabilan Igbo ya shugabanci Najeriya ba - Uwazuruike

- Ralph Uwazuruike yace mutanen arewa ba zasu taba yarda inyamiri ya zama shugaban kasa ba

- Shugaban kungiyar fafutukar neman Biafra MASSOB yace kawai mutanen Igbo su manta ce kujeran shugaban kasa

- Uwazuruike yace kai su fuskanci samo yancin Biyafara shine mafita

Mutanen arewa ba zasu taba yarda dan kabilan Igbo ya shugabanci Najeriya ba - Uwazuruike
Mutanen arewa ba zasu taba yarda dan kabilan Igbo ya shugabanci Najeriya ba - Uwazuruike

Mu’assasin kungiyar MASSOB, Chief Ralph Uwazuruike,yayi kira ga jama’an kabilar Igbo su manta da zancen dan kabillan Igbo ya zama shugaban kasa

Yace wannan dalili ne yasa wadanda zasu iya zama shugaban kasa irinsu Dr. Alex Ekwueme, and Chief Emmanuel Iwuanyanwu,na jam’iyyar PDP basu zama ba.

A wata jawabi da yayi ranan Litinin,6 ga watan Maris, Uwazuruike wanda diraktan labaran kungiyar, Mazi Chris Mocha ya wakilta a Umuaka, karamar hukumar Njaba a jihar Imo, ya nuna juyayinsa akan Ekwuweme da sauran shugabannin Igbo wadanda suka shaida yakin basasa wanda aka karashe akan kin jinin yan kabilan Igbo.

Shi kuma Ekwueme yace: “ Na kasance mataimakin shugaban kasa har shekarar 1983, kuma bis ga ka’idar jam’iyyar NPN, da nayi takaran shugaban kasa a 1987, amma aka kwace mulkin da karfin soja a 1983.

Na sake takara a shekarar 1998. A lokacin ne aka saki Obasanjo daga kurkuku kuma ya samu nasara a zaben bisa ga taimakon abokansa soji. Na sake takara a 2013, amma na sha kasa."

” Sai kawai na fara addu’a cewa sauran yan kabilan Igbo zasu cigaba daga inda natsaya”

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel