Likitoci sun ceto rayuwar wani Kunkuru ta hanyar tiyatan sulalla

Likitoci sun ceto rayuwar wani Kunkuru ta hanyar tiyatan sulalla

Likitoci a kasar Thailanda sun ceto rayuwar wani kunkuru a ranar Litinin 6 ga watan Maris baya wani aikin tiyatan ceton rai da suka yi masa inda suka ciro sulalla kusan guda dubu daya daga cikinsa, Tiyata irinsa na farko a Duniya.

Likitoci sun ceto rayuwar wani Kunkuru ta hanyar tiyatan sulalla
Likitoci sun ceto rayuwar wani Kunkuru ta hanyar tiyatan sulalla

Likitocin su biyar da jami’ar Chulalongkorn na garin Bangkok inda suka kwashe awanni 6 suna yi ma kunkurun aiki mai suna Omsin, inda suka ciro sulalla 915 da nauyinsu ya kai kilo 59. “Sulallan kasashe dayawane, yawanci daga kasashen gabashin duniya” inji likita Nuntarika Chanose yayin dayake yi ma manema labarai jawabi.

KU KARANTA: Karayar tattalin arziki: “Ku tuhumi tsofaffin gwamnoni ba Buhari ba” – Obasanjo

Likitoci sun ceto rayuwar wani Kunkuru ta hanyar tiyatan sulalla
Sulallan da aka ciro daga cikin Kunkurun

Mutane dake kasashen gabashin duniya, suna da al’adan jefa sulalla a cikin rafin da akwai kunkuru, inda suka camfa hakan na kawo sa’a, musamman yadda kunkuru ka iya kwashe shekaru 100 a rayuwa, wannan al’adar addinin Budha ne.

Kunkuru Omsin shekarunsa 25, kuma yana rayuwa ne a rafin Sriracha dake kudu maso gbashin birnin Bangkok, an kawo shi cibiyar adana kunkuru na rundnar sojin ruwa ne bayan mai shi ya daina kulawa da shi a watan yuni.

Likitoci sun ceto rayuwar wani Kunkuru ta hanyar tiyatan sulalla

A watan Feburairu ne likitocin dabbobi na jami’ar Bangkok suka bukaci a kawo Omsin don su yi masa aiki bayan sun lura yana iyo ne ta gefe daya kawai, ba tare da amfani da gefen hagunsa ba. “Da fari mun dauka rabin jikinsa ya mutu ne, amma da muka dauki hoto sa sai muka gano tarin karafa a cikinsa,” inji Nuntarika

“AIkin bana wasa bane, kuma akwai hatsari” inji likita Briksawan, Nuntarika ta kara da fadin. Bayan mun ciro sulallan ne sai muka fahimci kunkurun ya fara shaker iska yadda ya kamata.”

Likitoci sun ceto rayuwar wani Kunkuru ta hanyar tiyatan sulalla
Likitoci sun ceto rayuwar wani Kunkuru ta hanyar tiyatan sulalla

A yanzu dai kunkuru Omsin na jinya a asibitin, amma da zarar ya kammala hutawa zamu mayar da shi cibiyar sojojin ruwan, inda daga nan kuma zasu mayar da shi cikin ruwa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel