Jiragen ruwa 31 makare da kayayyakin masarufi na kan hanyar tashar jirgin ruwan Legas

Jiragen ruwa 31 makare da kayayyakin masarufi na kan hanyar tashar jirgin ruwan Legas

-Kimanin jiragen ruwa 31 ne makare da man fetur da dangoginsa da abinci da kuma sauran kayayyakin masarufi ke kan hanyarsu ta zuwa tashar jirgin ruwan Apapa da Tin-Can Island da ke Legas

-Wannan albishir ya fito ne daga bakin hukumar kula da tasoshin jiragen ruwa NPA a cikin wata mujallar mai bayyana irin jiragen da ake sa ran zuwansu tasoshin jiragen ruwan Najeriya.

Jiragen ruwa 31 makare da kayayyakin masarufi na kan hanyar tashar jirgin ruwan Legas
Jiragen ruwa 31 makare da kayayyakin masarufi na kan hanyar tashar jirgin ruwan Legas

Kimanin jiragen ruwa 31 ne makare da man fetur da dangoginsa da abinci da kuma sauran kayayyakin masarufi ke kan hanyarsu ta zuwa tashar jirgin ruwan Apapa da Tin-Can Island da ke Legas

Ana sa ran soma isowar jiragen ne daga ranakun yau Talata 7 zuwa Lahadi 19 ga watan Maris na shekarar 2017.

Jiragen ruwa 31 makare da kayayyakin masarufi na kan hanyar tashar jirgin ruwan Legas
Jiragen ruwa 31 makare da kayayyakin masarufi na kan hanyar tashar jirgin ruwan Legas

Wannan albishir ya fito ne daga bakin Hukumar kula da tasoshin jiragen ruwa na Najeria NPA, a cikin wata mujallarta ta harshen Turaci mai suna 'Shipping Position,' mai bayyana irin jiragen da ake sa ran isowarsu tasoshin jiragen ruwan Najeriya.

Kofen mujallar wacce ce kamfanin dillanci labarai na najeria NAN ya yi arba da ita a ranar Talata 7 ga watan Maris shekara ta 2017 a jihar Legas.

Kamfanin NAN ya ba da rahoton cewa, 6 daga cikin jiragen na dauke ne da man fetur da man dizel.

Yayin da hukumar kula da tsoshin jiragen ruwan ke cewa, sauran jirage 25 na dauke ne da alkama, da kayan masarufi, da sukari, da karafa, da Gishiri, da man amfanin yau da kullum, da dayen manja, da waken soya, da daskararren danyen kifi, da sauransu.

Mujallar hukumar ta kuma cigaba da cewa, wasu jiragen 21 tuni suna tashar jiragen ruwa a Legas a inda suke sauke wasu daga cikin muhimman kayyakin bukatu na yau da kullum.

A kwanankin baya ne kafinya tafi hutun duba lafiyarsa shugaba Buhari ke kira da 'yan Najeritya dasu kara hakuri dangane da matsin halin rayuwar da ake ciki, domin sauke na tafe a bisa tanadin da suka yiwa 'yan Najeriya.

Ga wani hoton bidiyon jin ra'ayin jama'a kan lafiyar shugaban Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel