Tagwayen da aka haifa a hade na fuskantar matsala mai tsanani shekaru 4 bayan an raba su, ana neman N5m don yi masu aiki (HOTUNA)

Tagwayen da aka haifa a hade na fuskantar matsala mai tsanani shekaru 4 bayan an raba su, ana neman N5m don yi masu aiki (HOTUNA)

Kyawawan tagwaye, Hassana da Hussaina, wanda aka haifa a hade a jihar Kano a shekarar 2013 sannan kuma daga baya aka rabasu a kasar India, na fuskantar matsala mai girma shekaru hudu bayan anyi masu aikin.

Tagwayen na fama da matsalar yoyon fitsari da kashi wanda hakan yasa a koda yaushe ana sanya masu zanen jarirai domin yak are kashi da fitsarin daga zuba a kasa.

Tagwayen da aka haifa a hade na fuskantar matsala mai tsanani shekaru 4 bayan an raba su, ana neman N5m don yi masu aiki (HOTUNA)

A cewar asibitin koyarwa na Aminu Kano, asibitin dake kula da su, yaran na bukatar kudi naira miliyan biyar (N5million) domin a magance masu matsalar.

KU KARANTA KUMA: Za'a iya samun gidan yankan kai a Kano — Ganduje

An hana su shiga da wasa da tsararrakinsu saboda matsalar.

Asibitin koyarwa na Aminu Kano sun saki wata sanarwa game da halin da tagwayen ke ciki a ranar Laraba, 1 ga watan Maris.

Tagwayen da aka haifa a hade na fuskantar matsala mai tsanani shekaru 4 bayan an raba su, ana neman N5m don yi masu aiki (HOTUNA)

Karanta sanrwan a kasa:

“An haifi wadannan kyawawan tagwayen a hade a asibitin kwararru na Murtala Muhammed Kano a shekarar 2013 daga baya aka mayar da su asibitin koyarwa na Aminu Kano. Daga baya kuma aka tura su kasar India don a raba su, shekaru hudu bayan anyi nasaran rabasu din sai suka fara fama da wani gagarumin matsala wanda ake bukatar naira miliyan biyar (N5,000,000:00) a asibitin da aka raba su.

“Hassana da Hussaina na fama da ciwon yoyon fitsari da kashi wanda a koda yaushe cikin sanya zanen jarirai suke don hana kashi da fitsrin zubowa a kasa. Wannan matsalar ta sa basa samun damar wasa da sauran yara a gida da makaranta.

“Iyayen tare da hadin gwiwar asibitin koyarwa na Aminu Kano, suna rokon jama’a da su taimaka su hada kudi don magance matsalar wadannan tagwayen.

“A tura dukka kudaden ga asibitin koyarwa na Aminu Kano ko kuma a kira sashin ta lambar wayan tarho 08065580007/08023088964 don Allah a taimaka, ku tura sakon gaba.”

Abun tausayi!

Asali: Legit.ng

Online view pixel