Yaro mai wankin takalmi a Borno ya yi wa dalibai fintinkau

Yaro mai wankin takalmi a Borno ya yi wa dalibai fintinkau

- Wani yaro mai wankin takalmi dan shekara 12 mai suna Ibrahim Bukar wanda ke zagawa a birnin Maiduguri yana wanke takalma don samun na abinci, ya yi wa yara fintinkau a wata makaranta a garin Maiduguri

- Sanadiyyar wani mutumin kirki a sa yaron a makaranta ganin halin da yaron ya shiga na maraici da kokarin ciyar da kansa da kuma mahaifiyar da sana'ar wankin takalmi

Yaro mai wankin takalmi a Borno ya yi wa dalibai fintinkau
Yaro mai wankin takalmi a Borno ya yi wa dalibai fintinkau a aji

Wani yaro mai wankin takalmi dan shekara 12 mai suna Ibrahim Bukar wanda mai zaman ke zagawa a birnin Maiduguri yana wanke takalma don samun na abinci, ya yi wa yara fintinkau a wata makarantar ,mai zaman kanta a cikin garin Maiduguri

Wannan ya biyo bayan sa shi a makaranta ne da wani mutumin kirki mai suna Ibrahim Yusuf ya yi sakamakon gamu da yaron da ya yi ya na ragaita don neman aiki a cikin garin.

Jaridar Daily Naigerina ta rawaito cewa, Ibrahim Bukar dan shekara 12 ya ce, shi ne ke kula da gidansu, duk abin da ya samu yana ba mahaifinsa ne a kullum daga wankin takalma.

Yusuf ya bayyana yadda ya gamu da yaron da kuma yadda ta kai a ak sa shi a makaranta da kuma irin kwazaon da ya nuna kamar haka;

Cikin tausayawa, Yusuf ya ce yaron ya kai shi gurin mahaifinsa sannan sai "Yaron ya kai mu gidansu a unguwar London Chiki, amma mu ka yi rashin sa’a mahaifin nasa ba ya nan.

"A ka ce mana mahaifinsa dan kasuwa ne, sai mu ka yanke shawarar mu je mu gan shi a wajen kasuwancinsa.

"A can din ma dai mahaifin na sa ba ya nan, amma kayayyakin da ya ke sayarwa su na nan, sai makwabtansa su ka ce ya je ya dawo. Yayin da mu ke jiran sa ne na fahimci dalilin da ya sa ba zai iya sa yaronsa a makaranta ba.

"Kimanin mintuna 45 mu na jira, a cikin minti 45 dinnan ba wanda ya zo sayen wake ko geron da ya ke sayarwa. A karshe bayan ya dawo, mu ka gaishe shi mu ka kuma fada masa abin da ya kawo mu.

"Mutumin ya kusa fashewa da kuka, ya fada mana cewa ya so 'ya'yansa su je makaranta, amma ba zai iya daukar nauyinsu ba.

Mahaifin nasa ya fada mana cewa, kafin rikicin Boko Haram ya yi kamari ya tura yaron makarantar allo a Dikwa, yayin da 'yan Boko Haram su ka kwace wajen, yaron ya gudo Maiduguri."

Malam Yusuf ya ce ba shi da zabi fiye da sa yaron a makarantar kudi saboda ba makarantar gwamnati a kusa da zai iya zuwa a kafa.

"Da taimakon wani mai taimakawa al'umma da nawa kokarin, yanzu Ibrahim yana karatu a wata makaranta mai suna Future Hope Private School da ke unguwar London Chiki a Maiduguri, kuma kawo yanzu ya na kokari sosai. Na ziyarci makarantar yau (Juma'a) don na gane wa idona halin da ya ke Chiki.

"Malamarsu ta fada min cewa, Ibrahim yana kokari fiye da yadda ake zato. Ta ce ya fada mata yana so ya zama dalibin da ya fi kowa a ajinsu, kuma kullum da yamma wani yaro makwabcinsa yana yi masa bita. Yanzu Ibrahim zai iya karanta harufan Turanci daga A zuwa Z, cikin mako daya kacal. Ya wuce sauran 'yan ajinsu a kokari," cewar Malam Yusuf.

Shugaban makarantar ya ce za a dinga ciyar da shi gaba gwargwadon kokarinsa da kuma bitar karatun da ya wuce shi a azuzuwan da ya tsallake.

Asali: Legit.ng

Online view pixel