‘Yan sanda 4 sun mutu a mumunan hadari

‘Yan sanda 4 sun mutu a mumunan hadari

Jami’an yan sanda na X-Squad jihar Legas sun rasa rayukansu a ranan Lahadi, 5 ga watan Maris sanadiyar wata mumunar hadari a bakin aiki.

‘Yan sanda 4 sun mutu a mumunan hadari
‘Yan sanda 4 sun mutu a mumunan hadari

Kakakin hukumar yan sanda na jihar, ASP Olarinde Famous-Cole, yace hadarin ya faru a hanyar Isiwu a Imota, kusa da Ikorordu jihar Legas, misalin karfe 1 na ranan.

Jawabinsa yace:

“Misalin karfe 1 na rana na Lahadi, wata motar yan sanda mai lamba NPF 409 D dauke da yan sanda 5 tacyi kicibis da wata babbar mota.

“Direban babbar motan ya arce da wuri bayan faruwan hadarin."

KU KARANTA: An saki Sadiq Zazzabi

“Yan sanda 3 su mutu a take. Wani ASP na yan sanda kuma wani Insfekto su jikkata sosai kuma an kaisu asibitin jami’ar jihar Legas, Ikeja, inda aka bayyana cewa aya daga cikinsu ya mutu."

Cole yace an ajiye gawawwakinsu a babban asibitin Ikorodu kuma za’a kaisu LASUTH domin bincike.

Yace motocin da da hadarin ya shafa an kaisu ofishin yan sanda da ke Ikorodu.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel