Shigowar yanzu: An yanke wa tsohon Gwamnan Adamawa hukunci

Shigowar yanzu: An yanke wa tsohon Gwamnan Adamawa hukunci

Yanzu yanzu labarin da ke iso mana yana nuni da cewa an yancewa tsohon gwamnan jihar Adamawa dake arewa maso gabas mai suna Bala Ngilari hukuncin dauri n shekara 5 a gidan yari.

YANZU-YANZU! An yanke wa tsohon Gwamnan Adamawa hukunci
YANZU-YANZU! An yanke wa tsohon Gwamnan Adamawa hukunci

A wani labarin kuma, Kotun daukaka kara da ke Yola Fadar jihar Adamawa, ta ba da hukuncin tsige tsohon gwamnan Murtala Hammayero Nyako da majalisar Dokoki ta yi, baya bisa ka’ida.

Da take gabatar da hukuncin, kotun mai Alkalai biyar da mai shari’a Jummai Hanatu Sankey ke shugabanci ta ce kotun ta yi watsi da tsigewar, kan hujjar keta hakkin tsohon gwamna Nyako na rashin ba shi damar kare kansa daga tuhumar da majalisar ke masa.

Kuma bisa ka’ida inji kotun kotun tilas ne ta mika masa takardar tuhumar hanu-da-hanu. Sharadin da majalisar ta kasa cikawa.

Sai dai sugunne bata kare ba inji kwamishina shara’a na jihar Adamawa, Barr. Silas Bala Sanga saboda majalisar dokokin jiha zasu daukaka kara zuwa kotun koli.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel