Raƙuma sun janyo mummunar hatsari a jihar Jigawa

Raƙuma sun janyo mummunar hatsari a jihar Jigawa

Wata mummunar hatsari ya wakana a ranar Asabar 4 ga watan Maris inda aka taho mu gama tsakanin gungun wasu rakuma da wata karamar mota kirar Golf a jihar Jigawa.

Anyi taho mu gama tsakanin Raƙuma da wata mota a jihar Jigawa
Anyi taho mu gama tsakanin Raƙuma da wata mota a jihar Jigawa

Rahotanni sun bayyana cewar hatsarin ya faru ne sakamakon shiga kan titi da rakuman suka yi da gudu, inda nan take wasu rakuma biyu daga cikinsu suka mutu, inda motar tayi kaca kaca ka mommole.

Amma zuwa yanzu ba’a tantance halin da direban motar yake ciki ba, sakamakon an yi gaggawar garzayawa da shi zuwa Asibiti.

Raƙuma sun janyo mummunar hatsari a jihar Jigawa
Raƙuma sun janyo mummunar hatsari a jihar Jigawa

KU KARANTA: “Zan dawo nan bada dadewa ba, in cigaba daga inda na tsaya” – inji Buhari yayin daya kira gwamna Yahaya Bello

Wannan lamari ya fusata ma mazauna unguwar da lamarin ya faru, in da gargadi makiyaya dasu dinga kulawa da dabbobinsu, saboda kiyaye faruwar haka a nan gaba.

Raƙuma sun janyo mummunar hatsari a jihar Jigawa
Raƙuma sun janyo mummunar hatsari a jihar Jigawa

A wani labara kuma hukumar kiyaye haddura ta kasa, FRSC reshen jihar Jigawa ta jaddada manufarta na tabbatar da bin ka’idodin tuki da manyan hanyoyi. Shugaban hukumar ne tabbatar da haka biyo bayan yawan haddura da ake samu a wasu yankunan jihar.

Raƙuma sun janyo mummunar hatsari a jihar Jigawa
Raƙuma sun janyo mummunar hatsari a jihar Jigawa

Raƙuma sun janyo mummunar hatsari a jihar Jigawa
Raƙuma sun janyo mummunar hatsari a jihar Jigawa

Jihar Jigawa na daya daga cikin jihohin dake matsawa sosai kan daukan mutane biyu a gaban mota.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel