An kashe mawallafin littafin tarihin Obasanjo a hanyar sa na dawowa daga bikin ranar haihuwa

An kashe mawallafin littafin tarihin Obasanjo a hanyar sa na dawowa daga bikin ranar haihuwa

- Adinoyi Ojo Onukaba ya mutu yayinda yake dawowa daga bikin zagayowar ranar haihuwar Obasanjo

- Yan iska ne suka kai hari ga mawallafin littafin rayuwar tsohon shugaban kasar

Adinoyi Ojo Onukaba wanda ya kasance mawallafin litaffin tarihin Obasanjo ya rasa ransa bayan ya dawo daga bikin cikar tsohon shugaban kasar shekara 80 a duniya.

A cewar Sahara Reporters, wasu yan iska ne suka kai ma Onuakaba, wanda ya kasance tsohon dan takaran gwamnan jihar Kogi a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) hari wanda hakan yasa mutarsa ta dunga juyawa a kan titi.

An kashe mawallafin littafin tarihin Obasanjo a hanyar sa na dawowa daga bikin ranar haihuwa

Wata majiya tace: “Yana kokarin tserewa daga wasu yan fashi ne a babban titin Akure lokacin da motarsa ta kufce masa, yana ta jujjuyawa sannan kuma ya mutu a take.”

Mummunan al’amarin ya afku ne a ranar Lahadi, 5 ga watan Maris yayinda yake dawowa daga bikin zagayowar ranar haihuwar Obasanjo an kuma sanar da iyalan sa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Osinbajo zai kai ziyara jihar Edo a safiyar nan

An kai gawarsa babban asibitin kwararru na jiha a Akure.

Ya kasance Manajan Daraktan Daily Times of Nigeria na karshe a karkashin shugaban kasa Obasanjo ya kuma kasance daya daga cikin yan takara 21 na neman kujerar gwamnan jihar Kogi.

A cewar jaridar The Punch, an rahoto cewa an kashe Sanata Bafemi Ohudu a wata arangama da yan fashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel