Hamshaƙan shuwagabanni sun halarci bikin buɗe katafaren cibiyar karatu ta Obasanjo

Hamshaƙan shuwagabanni sun halarci bikin buɗe katafaren cibiyar karatu ta Obasanjo

A ranar asabar 4 ga watan Maris ne aka yi bikin kaddamar da katafaren cibiyar karatu da nazari da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya gina duk a cikin shagulgulan murnan cikarsa shekaru 80 a rayuwa.

Hamshaƙan shuwagabanni sun halarci bikin buɗe katafaren cibiyar karatu ta Obasanjo
Bikin buɗe katafaren cibiyar karatu ta Obasanjo

Ita dai wannan cibiya da aka kashe mata biliyoyin nairori wajen gina ta an fara ginata ne a watan Mayu na 2005, mallakin Obasanjo ce dari bisa dari, kuma an gina ta ne a garin Abekuta na jihar Ogun, kuma tana dauke da kayan tarihi na musamman da suka haura 4000, littattafai guda 2,000,000 sai kuma takardu masu muhimmanci guda milyan 15 don taimaka ma dalibai da ma’abota bincike don karance karance da nazari, kamar yadda shugaba kwamitin amintattu na cibiyar Christopher Kolade ya bayyana.

Hamshaƙan shuwagabanni sun halarci bikin buɗe katafaren cibiyar karatu ta Obasanjo
Hamshaƙan shuwagabanni sun halarci bikin buɗe katafaren cibiyar karatu ta Obasanjo

Sa’annna kuma, cibiyar ta dauki sama da matasa 500 aiki, don gudanar da al’amuran yau da kullum.

KU KARANTA:‘Lallai yan Najeriya mu dage da addu’a kada Najeriya ta taɓarɓare kamar PDP’ – Obasanjo

Hamshaƙan shuwagabanni sun halarci bikin buɗe katafaren cibiyar karatu ta Obasanjo
Kofi Anan

Wasu daga cikin hamshakan mutane da suka halarci taron sun hada da mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, shugaban kasar Liberia Uwargida Ellen Sirleaf-Johnson, shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe, shugaban kasar Sierra Leone Ernest Koroma, tsohon shugaban kasar Cotonou Boni Yayi da tsohuwar shugaban kasa Malawi Joyce Banda.

Haka zalika tsohon sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Anan, tsohon shugaban kasar Ghana John Akuffor, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Ernest Shonekan, Abdulsalam Abubakar, Namadi Sambo, Asiwaju Bola Tinubu, Rabiu Musa Kwankwaso, Sule Lamido, Aminu Masari da sauran jiga jigan siyasar Najeriya.

Hamshaƙan shuwagabanni sun halarci bikin buɗe katafaren cibiyar karatu ta Obasanjo
Hamshaƙan shuwagabanni sun halarci bikin buɗe katafaren cibiyar karatu ta Obasanjo

Osinbajo yace “Baban Obasanjo mutum ne na daban, amfanin rubuta tarihi, guda biyu ne, na daya don amfanin kanka, na biyun kuma shine domin daukan darussa kwarara, dangane da matsalolin da aka fuskanta a baya, tare da hanyoyin magance su.”

Ita ma Sirleaf cewa tayi “ Tarihi ba zai manta da wannan taron ba, inda aka sanya tubalin adana tarihin nahiyar Afirka, don haka ya kamata duk sauran tsofaffin shuwagabannin kasa suma su dauki irin wannan mataki na tarawa da adana tarihi.”

Hamshaƙan shuwagabanni sun halarci bikin buɗe katafaren cibiyar karatu ta Obasanjo
Hamshaƙan shuwagabanni sun halarci bikin buɗe katafaren cibiyar karatu ta Obasanjo

Daga nan ta shawarci dalibai cewa “Dalibai yan Afirka da malaman su su dage su ga sun halarci wannan katafaren cibiyar karatu, kamar yadda muka yi a yau, domin sanin yadda daya daga cikin mashahuran yayan Afirka yayi rayuwa.”

Hamshaƙan shuwagabanni sun halarci bikin buɗe katafaren cibiyar karatu ta Obasanjo
Hamshaƙan shuwagabanni sun halarci bikin buɗe katafaren cibiyar karatu ta Obasanjo

Shima a nasa bayanin, Obasanjo yace tun a 1988 yake da burin gina wannan cibiyan karatu don tattara bayanai da muhimman takardun yakin basasa, inda yace “Gaba dayan mu mun kafa tarihi a yau” sa’annan ya gode ma gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun da tsohon gwamnan jihar Cif Olusegun Osoba kan rawar da suka taka.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel