“Jonathan ne ya hana ceto ýan matan Chibok” - inji ƙasar Birtaniya

“Jonathan ne ya hana ceto ýan matan Chibok” - inji ƙasar Birtaniya

Bayanai sun bayyana kan yadda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dakile yunkurin sojojin kasar Birtaniya wajen ceton yan matan Chibok su 300 da kungiyar Boko Haram ta sace.

“Jonathan ne ya hana ceto ýan matan Chibok” - inji ƙasar Birtaniya
“Jonathan ne ya hana ceto ýan matan Chibok” - inji ƙasar Birtaniya

Shahararriyar jaridar kasar Birtaniya ‘The Observer’ ce ta fasa kwai kan yadda sojojin kasar Birtaniya yayin wata shawagi da suka gudanar a Arewacin Najeriya suka gano takamaimen inda yan aka boye yan matan Chibok din da Boko Haram ta sace sun a watan Afrilun 2014.

Jaridar tace: “Jim kadan bayan sace yan matan ne Rundunar sojin Birtaniya ta gano inda aka boye su” kamar yadda wata majiya da suka gudanar da aikin na musamman ta bayyana mata. Majyar ta cigaba da fadin “Mun nemi daman ceto yan matan, amma gwamnatin Najeriya bata amince mana ba.”

KU KARANTA: ‘Lallai yan Najeriya mu dage da addu’a kada Najeriya ta taɓarɓare kamar PDP’ – Obasanjo

“Jonathan ne ya hana ceto ýan matan Chibok” - inji ƙasar Birtaniya
“Jonathan ne ya hana ceto ýan matan Chibok” - inji ƙasar Birtaniya

Haka dai sojojin suka cigaba da sanya idanu kan yan matan, yayin da kungiyar ta Boko Haram ta fara rarrana su rukuni rukuni. Wasu takardun bayan taron daya gudana tsakanin jami’an gwamnatin Najeriya dana Birtaniya ya nuna cewar gwamnatin Najeriya tayi watsi da duk wani tayin da aka yi mata na ceto yan matan.

“Wannan matsalar Najeriya ne, don haka dole ne a kyale hukumomin tsaron mu su shawo kan matsalar.” In ji tsohon shugaban kasa Jonathan yayin wata ganawa da yayi da jakadan kasar Birtaniya a nahiyar Afirka Mark Simmonds a ranar 15 ga watan Mayu na 2014.

Bugu da kari wasu takardun bayanai sun tattara yadda tattaunawa tsakanin tsohon mashawarcin tsohon shugaban kasa kan harkokin tsaro Sambo Dasuki da mataimakin sakataren harkokin kasashen wajen na kasar Birtaniya James Duddridge, inda ya shaida ma gwamnatin Najeriya cewa sun sanya yan Boko Haram a tsakiya, kuma suna da dama ceto yan matan.

Har ila yau, wasu takardun sun nuna wani zaman tattaunawa daya gudana tsakanin Goodluck Jonathan da babban jami’i a rundunar sojin kasar Birtyaniya Manjo Janar James Chiswell, inda Jonathan din ya nuna damuwarsa da yadda wasu kasashen waje ke neman shiga lamurran Najeriya.

Idan za’a iya tunawa, Goodluck Jonathan ya sha kakkausan suka ta yadda dangane da satar yan matan, musamman bayan ya soki kungiyar nan dake karajin a sako mata yan matan wato Bringbackourgirls, shima gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya caccaki Jonathan a fili, inda ya nuna bacin ransa da rashin kirarsa da Jonathan yayi, har sai bayan kwanaki 19 da sace yan matan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel