Yadda na hadu da miji na Inji matar Gwamna

Yadda na hadu da miji na Inji matar Gwamna

– Uwargidar sabon Gwamna Jihar Ondo Misis Akerodolu tace ba kudi ta bi lokacin da ta ga mijin na ta

– Misis Akeredolu tace ta hadu ne da Mijin na ta lokacin suna aikin bautar kasa

– Uwargidar Gwamna Akerodolu tace tana ganin dan saurayi tace wannan da shi za ayi

Yadda na hadu da miji na Inji matar Gwamna
Yadda na hadu da miji na Inji matar Gwamna

Uwargidar Rotimi Akeredolu wanda aka rantsar a matsayin sabon Gwamnan Jihar Ondo ta bayyana yadda suka hadu da mai gidan ta a wata hira da tayi. Misis Akeredolu tace ba wai kudi ta tsaya bi ba a lokacin da Rotimi Akeredolu ya fara neman ta.

Ko da yake dai ba Bayarabiya bace amma soyayya ya shiga tsakani lokacin da suke aikin hidimar kasa a Garin Enugu. Matar Gwamnan tace tana ganin sa a wancan lokaci ta fadawa kawayen ta cewa ta fa samu mijin aure.

KU KARANTA: Ana zalunci a mulkin Buhari Inji Sanata Shehu Sani

Yadda na hadu da miji na Inji matar Gwamna
Yadda na hadu da miji na Inji matar sabon Gwamna

Misis Betty Akeredolu dai Inyamura ce, sun kuma samu haihuwar ‘ya ‘ya har 4 da Gwamnan. Misis Akeredolu tayi fama da cutar nan ta ‘cancer’ na mama a baya. Tuni yanzu ta murmure, har ta bude Kungiya mai kula da irin wannan cuta.

Betty Akeredolu wanda yanzu tana da jika tace Mijin na ta mutum ne mai saukin kai kuma mai koshin lafiya. Sannan kuma Uwargidan Gwamnan ta bada shawara kuma ga ma’aurata.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel