Rundunar sojin Najeriya ta fittitiki yan Boko Haram daga Chikun gudu

Rundunar sojin Operation LAFIYA DOLE ta kare fitittikan yan tada kayar bayan Boko Haram a jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya inda suka fitini mutane.

Kakakin hukumar sojin Najeriya, Birgediya Janar Sani Usman Kukusheka ya bayyana hakan ne a shafin sada ra’ayinsa ta Fezbuk.

Karanta jawabin:

"Rundunar sojin 8 Task Force Division, karkashin rundunar Operation LAFIYA DOLE a yankin Arewa maso gabas tayi arangama da yan ta’addan Boko Haram jiya a Chikun Gudu, arewacin jihar Borno.

Bayan anyi musayan wuta da artabu, an kasha yan Boko Haram da dama kuma wasu un jikkata. Kana kuma an kwato motoci, makamai da harsasai.

Rundunar sojin ta kwace motoci yaki Toyota 2, wanda suka sace daga hannun jami’an tsaron kasar Nijar, Toyota Hilux, wanda suka kwace daga hannun rundunar 153 Task Force Battalion kwanakin baya, Babura kiran Yamaha guda 25, na’urar Sola, da kuma carbin harsasai.

Sauran sun kunshi bindiga mai kai biyu, kayan Boko Haram 12, Tuta 5, Harsasshi mai carbi 37, Alkur’ani 37 da litattafai 270.

Kana rundunar sojin sun kwace kuma sun kona Babura 70 da yan ta’addan ke amfani da shi wajen kai hari, shagunan magani 3 cike da magunguna, shaguna 3 na kayan masarufi da kuma jirgin ruwa 3.

Sun kwato takardan lasisin tukin mota na kasar Nijar 2, wayan sadarwa 2 da allo 2. Amma, jami’an soji 4 sun raunana kuma an kaisu asibiti domin jinya.

Mungode sosai"

Brigadier General Sani Kukasheka Usman

Kakakin hukumar sojin Najeriya

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel