Mummunan rikici tsakanin 'yan sanda da jam'iyyar APC

Mummunan rikici tsakanin 'yan sanda da jam'iyyar APC

Zaben kananan hukumomi da aka yi a jihar Taraba ya bar baya da kura inda jam'iyyar adawa ta APC ke zargin 'yan sanda da yin ba daidai ba. Jam’iyar ta yi zargin cewa an yi amfani da wasu manyan jami’an 'yan sandan jihar wajen aringizon kuri’u da hakan ya baiwa jam’iyar PDP dake mulkin jihar nasara.

Mummunan rikici tsakanin 'yan sanda da jam'iyyar APC
Mummunan rikici tsakanin 'yan sanda da jam'iyyar APC

To sai dai kuma rundunan 'yan sandan jihar ta musanta zargin da ake yi mata.

Bayan zaben kananan hukumomi da aka yi a jihar Taraban takaddama ta kunno kai tsakanin hukumar 'yan sandan jihar da jam'iyyar adawa ta APC .

Alh. Sani Chul shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC a jihar Taraban a wajen wani taron manema labarai, ya yi zargin cewa a zaben da aka yi a wasu kananan hukumomin jihar an ga jami’an 'yan sanda wato DPOs na tallafawa jam’iyar dake mulki, zargin da rundunan 'yan sandan jihar ta musanta.

KU KARANTA: Muhimmin sako daga Osinbajo

Sani Chul,ya ce jam’iyar ba za ta lamuncewa abun da ya kira aringizon kuri’un da suke zargin aka yi ba, wanda ya baiwa jam’iyar PDP dake mulkin jihar nasara.

To sai dai kuma ASP,David Misal kakakin 'yan sandan jihar ya kwatanta wannan zargi a matsayin labarin kanzon-kurege.

Haka nan ita ma dai Jami'iyyar PDP ta yi watsi da zargin. Alhaji Inuwa Bakari wanda shi ne jami’in hulda da jama’a na jam’iyar PDP a jihar Taraban ya ce zafin kaye ne ke sa shugabanin APC irin wannan zargi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel