An gano hukumomin kwastam da cin hanci dumu-dumu

An gano hukumomin kwastam da cin hanci dumu-dumu

Kwamitin da ke bai wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, shawara kan yadda za a yaki cin hanci da rashawa, ya ce har yanzu ana tafka almundahana a kasar ba tare da tunanin ukubar da ka iya biyo baya ba.

An gano hukumomin kwastam da cin hanci dumu-dumu
An gano hukumomin kwastam da cin hanci dumu-dumu

Shugaban kwamitin, Farfesa Itse Sagay, ya ayyana hukumar Raya Yankin Neja Delta NDDC, da Hukumar Hana Fasa Kauri ta Najeriya Custom, a matsayin hukumomin da har yanzu cin hanci da rashawa ya yi wa katutu.

A wani taron tattaunawa kan batun cin hanci da rashawa da aka yi a fadar gwamnatin Najeriyar ranar Alhamis, kwamitin ya bayyana halin da ake ciki a yaki da cin hanci da rashawa a yanzu haka.

KU KARANTA: Ana shirin kafa sabuwar PDP

Farfesa Sagay ya ce duk da matsin tattalin arzikin da kasar ke ciki, hukumar raya yankin Neja Delta ta sayi motoci guda 70.

Takwas daga cikin motocin kirar Jif ne samfurin Lexus, inda ta sayi ko wacce daya kan Naira miliyan 70, wanda jumlarsu ta kama naira miliyan 560.

Mista Sagey ya ce duk da sayen motocin da hukamar ta yi, shugaban NDDC din ya yi korafin cewa hukumar ba ta da kudin da za ta aiwatar da wasu ayyukanta.

Dangane da hukumar kwastam kuma, Mista Sagay ya ce babu wani sauyi da aka samu a hukumar kan yadda ta ke gudanar da aikinta, kafin da kuma bayan 29 ga watan Mayun 2015.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel