Ta fatattaki mijinta bayan kwashe shekaru 6 ba tare da ya biyata sadakin aure ba

Ta fatattaki mijinta bayan kwashe shekaru 6 ba tare da ya biyata sadakin aure ba

Wata mata mai suna Felicia Akinshola ta roki wata kotun majistri a jihar Nassrawa da tayi wa Allah ta raba aurenta da mijinta Akin Akinsola saboda ya gagara biyan sadakinta sama da shekaru 6 suna tare.

Ta fatattaki mijinta bayan kwashe shekaru 6 ba tare da ya biyata sadakin aure ba
Ta fatattaki mijinta bayan kwashe shekaru 6 ba tare da ya biyata sadakin aure ba

Felicia tace “Akin bai biya sadakin aurena nab a kamar yadda al’adan yarabawa ta tanadar, kuma duk kokarin da nayi ya biya sadakin yaci tura. Akin mutum ne mara kirki, baya biyan kudin makarantan yayanmu.

“Ko abinci mai kyau baya bamu a gida, idan kuma bani da lafiya, Akin ko a jikinsa, baya tausaya min. wadannan halayyan nasa ya sanya duk ya sire min a rai, don haka nake rokon kotu data raba auren mu.”

KU KARANTA: Ba muyi tsammanin tafiyar Buhari zata daɗe haka ba’ – APC

Bugu da kari Felicia mai shekaru 34 tana da yara 3 tare da Akin, don haka ta bukaci kotu data bata damar kwashe yaran don basu kulawar data dace, sakamakon ubansu ballagaza ne.

Sai dai a nasa barayin, Akin ya roki kotu data basu damar sulhuntawa a wajen kotu, inda ya bukaci kotu data dan bashi lokaci don tattaunawa da matarsa da sauran danginsa kan batun, ko za’a shawo kan lamarin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel