Manyan kalamai 5 na shugaban kasa Buhari a 2016

Manyan kalamai 5 na shugaban kasa Buhari a 2016

A lokaicin yakin neman zabe, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya alkawarin tabbatar da daidaitar kasar kan hanya mai inganci da saurarrakinsu.

Amma a yanzu kuma wasu ‘yan Najeriya da dama suna kallon dukkanin alkawuran da shugaban ya yi, kamar sun tsaya ne kawai a siyasance.

Manyan kalamai 5 na shugaban kasa Buhari a 2016

Ga wasu daga cikin manyan kalaman da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a shekarar 2016.

1. Zama a Fadar ‘Aso Rock’ sai sa ni mantawa da halin da talakawa ke ciki ba

Ina sane da manyan matsalolin da ‘yan Najeriya suke fuskanta a watannin nan. Zaman da nake yi a nan cikin fadar shugaban kasa a Abuja bai sa na shantake, tare da mantawa da halin da ‘yan’uwana talakawa da sauran ‘yan Najeriya suke ciki ba.

Musamman matsin tattalin arziki, rashin ayyukan yi da sauransu. Amma ina tabbatar mana da cewa wadannan matsalolin na wucin gadi ne, da yardar Allah za mu tsame kasarmu daga cikin su.

2. Ina son zama shugaban mai cika alkawuransa

A lokacin da na gabatar da kaina a gare ku a matsayin dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC kuma na nemi ku zabe ni, na yi alkawarin zama shugaban da zai cika alkawarinsa, sannan shugaban da zai zama abin dogaro ga wadanda suka zabe shi. Kuma wanda zai yi aikinsa tukuru. Don haka ina kan bakata, kuma da yardar Allah zan cimma muraduna.

3. Da sannu ‘Yan Najeriya za su amfana da muradun da muke shimfidawa a yanzu

Ina mai tabbatar wa dukkanin ‘yan Najeriya cewa nan gaba kadan, kowa zai amfana da kyawawan muradun da muke dora kasar nan a kai, bayan tsarkake ta da muke yi a yanzu.

4. Ba zan yi barci mai dadi ba, har sai na ga mun kawar da rikicin Boko Haram

Ina mai tabbatar muku da cewa wannan gwamnatin ba za ta tankwashe kafa ta huta ba, har sai ta kawar da rikicin Boko Haram baki dayansa, tare da sauran rikice-rikicen da ke addabar ‘yan Najeriya a yau.

5. Dole ministocina su tabbatar ‘Yan Najeriya sun ga canji mai ma’ana

Najeriya tana bukatar mazaje masu amsa sunansu don gudanar da ayyuka a fannoni daban-daban. Don haka na hori ministocina da su tabbatar ‘yan Najeriya sun ga canji mai ma’ana daga gare su. Sannan su tabbatar sun ba mara da-kunya a cikin ayyukansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel