Fusataccen ango ya kori amaryarsa washegarin auren yawa da akayi a Kano

Fusataccen ango ya kori amaryarsa washegarin auren yawa da akayi a Kano

Habiba Inusa ta kasance daya daga cikin wadanda suka amfana daga auren yawa a jihar Kano wanda aka gudanar a ranar Lahadi, 26 ga watan Fabrairu. Ta yi nasaran boye cikin ta daga mijin nasa sannan ta haihu washegarin auren.

Fusataccen ango ya kori amaryarsa washegarin auren yawa da akayi a Kano

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Habiba ta shiga nakuda washegarin auren sannan ta haifi da namiji. Wannan ya sa mazauna yankin Gangare na karamar hukumar Doguwa cikin jimami a matsayinsu na wadanda suka shirya bikin.

KU KARANTA KUMA: Matashi mai Cutar ciwon shan inna ya sha alwashin zama shugaban kasar Najeriya (hoto, bidiyo)

Angon Habiiba, Babangida ya kori ta da yaron daga gida saboda ba shine yayi mata cikin ba.

Aminu Daurawa, kwamandan hukumar Hisbah ta Kano, yace an tantance ma’auratan sosai, kuma anyi masu gwaje-gwajen lafiya da sauran abubuwa kafin auren.

Lokacin da aka nemi yayi magana kan al’amarin Habiba, yace: “An bukaci mu kawo sunayen ma’aurata watanni shidda bayan mun tantance su a hukumar kiwon lafiya ingantacce na ma’aikatar lafiya. Gwamnati ta yanke shawarar barin kananan hukumomi rikon al’amarin. Don haka komai na iya faruwa.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel