Sojoji sun dura gidan wani shugaban ‘Yan Shi’a

Sojoji sun dura gidan wani shugaban ‘Yan Shi’a

Sojoji sun dura gidan wani shugaban ‘Yan Shi’a
Yan Shi’a suna taro

Wasu sun raunata yayin da aka samu wani arangama tsakanin Sojoji da ‘Yan Shi’a a Garin Katsina. 'Yan Shi'an sun ce ba yau aka fara masu wannan ba.

Mutane 3 sun samu rauni yayin da wasu Sojoji suka dura gidan wani shugaban shi’a a Jihar Katsina. A yau din ne dai Sojoji suka dura gidan wani shugaban mabiya addinin Shi’a Sheikh Yakubu Yahaya.

Shugaban mabiyan na Shi’a Sheikh Yakubu Yahaya ya bayyanawa Jaridar Daily Trust cewa ba shakka Jami’an tsaro sun kai masu hari har suka raunata wasu dama. Ciki dai akwai wanda ya karya hakora, wasu kuma suka samu raunuka dabam-dabam a hannuwa.

KU KARANTA: Sojoji sun mamayi 'Yan Shi'a a Katsina

‘Yan Shi’an dai sun ce Jami’an tsaron sun zo ne da niyyar kisan gilla kamar dai yadda aka addabe su tun kwana biyu da suka wuce. Mai magana da bakin ‘Yan Shi’an yace Sojojin sun kai masu irin wannan hari a Garin Jos kwanaki. Jami’in ‘Yan Sanda na yankin ya dai ce za ayi bincike game da lamarin amma har yanzu shiru.

Farkon makon nan Femi Falana SAN Lauyan shugaban kungiyar IMN Ibrahim Az-Zakzaky, ya rubuta wasika ga Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo SAN da kuma Ministan shari’a na kasar Abubakar Malami SAN game da cigaba da daure malamin. Falana yace idan har gwamnati ba ta saki Zakzaky ba zai dauki mataki.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel