Tattaunawa da 'yan Boko Haram a kan 'yan matan Chibok zai iya haifar da zaman lafiya a Najeriya – Inji wani matsakanci

Tattaunawa da 'yan Boko Haram a kan 'yan matan Chibok zai iya haifar da zaman lafiya a Najeriya – Inji wani matsakanci

Wani matsakanci kuma lauya ya bayyana cewa neman ceto sauran ‘yan matan makarantar Chibok 195 a hannun ‘yan boko Haram zai iya haifar da zaman lafiya.

Tattaunawa da 'yan Boko Haram a kan 'yan matan Chibok zai iya haifar da zaman lafiya a Najeriya – Inji wani matsakanci
Tattaunawa da 'yan Boko Haram a kan 'yan matan Chibok zai iya haifar da zaman lafiya a Najeriya – Inji wani matsakanci

A tattaunawa tsakanin gwamnatin Najeriya da Boko Haram a kan sakin wasu 'yan mata 200 da aka sace daga Chibok kusan shekaru uku da suka wuce, wani matsakaici ya ce, tattaunawar zai iya bada wata daman sulhu da ‘yan ta’addan da kuma kawo zaman lafiya a rikicin arewa maso gabashin.

A watan Oktoba ne ‘yan Boko Haram ta sake 21 a cikin 'yan mata 220 da aka sace a watan Afrilu 2014 daga arewacin garin Chibok bayan shiga tsakani da kasar Switzerland da kwamitin Red Cross na kasa da kasa (ICRC) ta yi.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun kubutar da mutane 7,896 daga hannun Boko Haram

Wani matashi kuma lauya Zannah Mustapha ya ce tattaunawar da kungiyar, wanda suka haddasa hare-haren ta’addanci shekaru 7 da ta gabata don kafa shari’an musulunci a arewa maso gabashin Najeriya, dole ne a nemi wata hanyar sasantawa bayan ceto sauran 'yan matan makarantar Chibok 195 da sun kasance a sansanin Boko Haram yanzu.

Shugaba Buhari ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa zai iya kokarinsa ganin ‘yan matan Chibok sun sake saduwa da iyalansu, kuma gwamnati ta ce ‘yan Boko Haram na shirye don tattaunawa da ita.

Matsakanci kuma lauya Zannah Mustapha ya bayyana aka a lokacin da ya ke tattaunawa da kungiyar Thomson Reuters Foundation.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel