Sojan kasar Amurka ya musulunta bayan wata mukabala

Sojan kasar Amurka ya musulunta bayan wata mukabala

Michael Barnes ya girma a matsayin mabiyi addinin kirista a Alexandria, Louisiana. Ya shiga aikin soja yana da mai shekara 23.

Sojan kasar Amurka ya musulunta bayan wata mukabala
Sojan kasar Amurka ya musulunta bayan wata mukabala

Lokacin da aka turasu kasar Jamus domin aiki, ya hadu da wani Sojan Amurka musulmi wanda ya kasance yana ma mutane da’awah akan musulunci.

Ashe wannan abu na baiwa Michael Barnes haushi. Wata rana sai ya kalubalancesa cikin jama’a har suka fara muhawara akan musulunci da Kiristanci. Sauran sojin 30 sun shaida mukabalan.

KU KARANTA: Majalisa zatayi bincike kan batan kudi 5.1trn

Ba tare bayani filla-filla akan mukabalan da sukayi ba Michael Barnes yace : “ Soja musulmin yayi mini bayani filla-filla game da addininsa tamkar ya sihirce ni, yayi mini bayanin musulunci fiye da abinda nike tsammani. Na kasance ina tunanin cewa ina rike da gaskiya amma yau nayi mamakin abinda na saurara."

Bayan an kammala mukabalan , Michael Barnes ya fara karatu akan addinin musulunci. Kulli yaumin sai ya karanta Alkur’ani da Bible. Bayan shekaru biyu na bincikensa sai ya furta Kalmar shahada kuma ya canza sunansa zuwa Khallid Shabazz.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel