Cutar masassarar Lasa ta sake bulla a Arewa

Cutar masassarar Lasa ta sake bulla a Arewa

- Mahukunta a jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya sun kebe mutane 38 sakamakon bullar cutar zazzabin Lassa a kauyen Zabarmari da ke karamar hukumar Jere

- Kwamishin lafiya na jihar Dr Haruna Mshelia, ya tabbatarwa da BBC cewa sakamakon gwajin samfurin jinin wata mata mai shekara 32 daga kauyen Zabarmari bayan ta kamu da zazzabi mai zafi a makon jiya ne , ya nuna cewa tana dauke da kwayar cutar ta Lassa

Cutar masassarar Lasa ta sake bulla a Arewa
Cutar masassarar Lasa ta sake bulla a Arewa

Kwayar cutar zazzabin na Lassa na janyo zubar jini ga wanda ya kamu da ita, kuma beraye ne ke yada ta ga bil'adama ta hanyar kashi ko fitsarinsu da kan taba kwanuka ko abinci.

Dr Mshelia ya bayar da tabbacin cewa ma'aikatar lafiya ta jihar ta ankarar da masu ruwa da tsaki da suka hada da shugabannin addinai da na al'ummar yankin, a kan su wayar da kan jama'a game da muhimmancin tsaftar muhalli da ta abinci.

KU KARANTA: Osinbajo ya fadi babbar matsalar Najeriya

Ya ce ya zuwa yanzu matar ta fara samun sauki, don kuwa tuni an dora ta a kan magunguna, kuma ana ba ta kulawar da ta dace a wurin da aka kebe ta.

Ya kuma ce za a fara aikin feshin magungunan kashe beraye da makamantansu a daukacin yankin ranar Alhamis.

Cutar zazzabin Lassa dai ta samo asali ne daga garin Lassa na karamar hukumar Askira Uba a jihar Bornon, lokacin da wasu bakin turawa suka fara kamuwa da ita shekara sama da arba'in da suka gabata.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel