An rufe matatar mai ta garin Warri (Dalili)

An rufe matatar mai ta garin Warri (Dalili)

- Hukumar da ke kula da harkokin mai ta kasa watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) a jiya ta sanar da rufe babbar matatar mai dake garin Warri

- Hukumar ta Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) tace hakan ya zama dole ne saboda wasu yan gyare gyare da za'a yi da kuma wasu matsalolin da suka taso

An rufe matatar mai ta garin Warri (Dalili)
An rufe matatar mai ta garin Warri (Dalili)

Shugaban matataun mai na NNPC din Mr. Anibor Kragha ne ya bayyana haka a Abuja inda kuma yace yanzu haka dai matatun man dake Fatakwal da Kaduna ne kawai ke aiki.

KU KARANTA: Baraka tsakanin magoya bayan Buhari da Osinbajo

A wani labarin kuma, Shugaban majalisar dattijan Najeriya Sanata Bukola Saraki ya umurci kwamitin majalisar da ke sa'ido kan harkokin man fetur da albarkatun kasa watau committee on Petroleum (Downstream) da ya binciki hukumar gudanar wa ta Nigeria National Petroleum Corporation (NNPC).

Sanata Saraki yace yakamata kwamitin ya binciki Nigeria National Petroleum Corporation (NNPC) kan bacewar da zunzurutun kudi har sama da N5 tiriliyan. Tayi a ma'aikatar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel