Amarya ta maka maigidanta gaban kotu saboda ya gaza ciyar da matansa 3 da ýaýa 9

Amarya ta maka maigidanta gaban kotu saboda ya gaza ciyar da matansa 3 da ýaýa 9

An gurfanar da wani magidanci gaban kuliya, inda yake fuskantar hukuncin dauri bayan ya kasa daukan dawainiyar matayensa guda uku da yayansa su tara.

Amarya ta maka Maigidanta gaban kotu saboda ya gaza ciyar da matansa 3 da ýaýa 9
Amarya ta maka Maigidanta gaban kotu saboda ya gaza ciyar da matansa 3 da ýaýa 9

Amaryar magidancin ne ta shigar da mijin nata kotu inda ta shaida ma kotun cewar mijin nasu mai suna Kudakwashe Maregedze mai shekaru 35 ya haifi yara 4 da matarsa ta fari, Uwargida Rachael Lunga, kuma yana da yaya 4 da Jesca Rudzayi sai kuma ita mai kara Sophia Jiri tana da da guda.

Amaryar Sophia Jiri ta bayyana ma kotu bukatarta na cewa tana bukatar dalan Amurka 206 ($206) a duk wata don kulawa dad anta guda daya mai shekaru 6, Sophia Jiri ta cigaba da bayyana ma Alkali cewar mijin nata Maregedze bai taba kashe ko kwandala ba game da dawainiyar yaron nata, inda tace wannan shine dalilin daya sat a shigar da kararsa gaban kotu.

KU KARANTA: Ýan bindiga sunyi garkuwa da malaman makaranta, sun buƙaci N30m

Shima Alkali mai shari’a Tinashe Tashaya bayan ya saurari karar ya umarci Maigida Maregedze daya biya amarya Sophia dalan Amurka 120 ($120) a kowane wata don kulawa da yaron nata ba tare da bata lokaci ba.

“Dole ne ka sanya mata $120 a asusun bankinta a kowane wata, wata kila wannan ka iya hanaka dibga ma matayenka ciki yadda kakeso. Dama dai ace suma sauran matayen naka guda biyu su kawo ka kara gaban kotu na, don na fahimci kamar baka da mutunci.” Inji Alkalin.

Daga karshe Alkalin kotun ya umarci Maigida Maregedz daya yi maza maza ya nemi aikin yi ba tare da bata lokaci ba don kulawa da sauran iyalansa, idan ba haka kuwa zai sa a kama shi, kuma a tuhume shi da laifin haihuwar yara rututu ba tare da basu kulawa ba.

Dayake kare kansa Maigida Maregedze yace shi fa $10 yake samu a wata sakamakon bashi da aikin yi.

“Ya Alkali mai shari’a, yayan 8 tare da matana 2, sai guda tare da amaryata data kawo ni kara. Dukkaninsu suna bukatar in kula dasu, amma bani da aiki.” Inji Maregedze yayin dayake magiya gaban kotu tare da nuna ma kotu takardun shaidun haihuwar yayan nasa 9.

Sai dai duk da magiyar da Maregedze yayi ma kotu, Alkali nai canza hukuncinsa ba, wanda hakan ke nufin dole sai ya dinga biya amarya Sophia Jiri $120 duk wata don kulawa da yaronta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel