Hukumar EFCC ta kama Abdulkarim Usman kan laifin damfara

Hukumar EFCC ta kama Abdulkarim Usman kan laifin damfara

A yau Laraba, 1 ga watan Maris, hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa wato EFCC, ta gurfanar da wani mutumi mai suna Abdulkarim Usman na 2 Biu, Badarawa Kaduna a gaban alkalin babban kotun tarayya dake Abuja, S L Shuaibu kan laifukan damfara guda uku.

A cewar bayanai daga shafin Facebook na hukumar ta EFCC, Abdulkarim Usman ya damfari wani Mukhtar Sani da Taufiq Mohammed Kailani a wasu ciniki daban-daban wanda gaba daya ya kai sama da naira miliyan biyu da dubu dari biyar (N2, 500,000.00).

Hukumar EFCC ta kama Abdulkarim Usman kan laifin damfara

Sun kara da cewa, Sani ya zargi Abdulkarim kan cewa a cikin shekarar 2016, Usman ya tunkare shi kan siyan mota kirar Honda V6 daga Kwatano, Jumhuriyyar Benin. Bayan sunyi cikini sai suka daidaita, mai korafin ya tura kimanin naira miliyan biyu (N2, 000,000) daga asusun bankin sa zuwa ga asusun bankin wanda ake kara. Amma Usman bai kawo masa mot aba kuma sannan bai dawo masa da kudin sa ba.

KU KARANTA KUMA: EFCC na neman wata mata ruwa a jallo kan laifin damfara

Yayinda bincike cikin al’amarin, wani daban ya kuma kawo kara a kan Abdulkarim wanda ake zargin sun hada kai da dan uwansa, Inusa Abdulkarim gurin damfarar Taufiq Kailani Mohammed, inda suka damfare shi kimanin naira dubu dari biyar da casa’in da uku (N 593,000) bayan ya yaudare shi da cewa ya samu kwangila da hukumar NCC don ya dunga odo masu man injin.

Sai Taufiq Mohammed ya tura ma Abdulkarim kudi ta hannun daya daga cikin kannensa mata amma har yanzu yaki biyan sa kudin sa.

Wanda ake zargin ya amsa laifukansa lokacin da aka karanto masa sannan kuma mai shari’a, Saidi Joshua ya bukaci kotu da ta sanya ranar da za’a fara sauraran kara yayinda hukumar tsaro suka nemi aba da beli wanda kotu tayi watsi da haka.

Mai shari’an ya daga sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Maris na 2017, yayinda ya bukaci a ci gaba da tsare mai laifin a kurkuku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel