Obasanjo ya raba ma makarantun firamari kyautan littafan labaran tatsuniyoyi

Obasanjo ya raba ma makarantun firamari kyautan littafan labaran tatsuniyoyi

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kai kyaututtukan littattafan labaran tatsuniyoyi ga wasu zababbun makarantun firamari duk a cikin shagulgulan bikin cikarsa shekaru 80.

Obasanjo ya raba ma makarantun firamari kyautan littafan labaran tatsuniyoyi
Obasanjo ya raba ma makarantun firamari kyautan littafan labaran tatsuniyoyi

Shi da kansa Obasanjo ne ya rubuta littafan labaran tatsuniyoyin, wadanda ya raba su ga wasu makarantun kudi da na masu zaman kansu dake karamar hukumar Ifo na jihar Ogun.

KU KARANTA: Amina Mohammed ta lissafa bangarori 11 da majalisar dinkin duniya zata fi baiwa fifiko

An sanya ma bikin rarraba littattafan take ‘Zangon tatsuniya tare da Baba a Ibogun’, inda dalibai suka bada labaran tatsuniyoyi daban dabana tare da gudanar da wasan kwaikwayo, an zabo daliban ne daga makarantun firamari daban daban da suka hada da Baptist Day school, Ewupe, Baptist Primary school, Ibogun, Beryl Chrysolite school da kuma Olusegun Obasanjo Academy Centre.

Obasanjo ya raba ma makarantun firamari kyautan littafan labaran tatsuniyoyi
Obasanjo ya raba ma makarantun firamari kyautan littafan labaran tatsuniyoyi

Obasanjo ya samu rakiyar uwargidarsa Bola, tare da shakikansa, kuma yayi amfani da daman wajen shawartan daliban dasu jajirce wajen yin karau tare da sanya ma kawunan sha’awar karance karance.

Shima shugaban kwamitin shirya taron bikin cikar Obasanjo shekaru 80, Farfesa Peter Okebukola ya bayyana tsohon shugaban kasar a matsayin hazikin marubuci, inda yace a yanzu haka yana da litattafai da dama daya rubuta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel