Amina Mohammed ta lissafa bangarori 11 da majalisar dinkin duniya zata fi baiwa fifiko

Amina Mohammed ta lissafa bangarori 11 da majalisar dinkin duniya zata fi baiwa fifiko

Hajiya Amina Mohammed sabuwar mataimakiyar sakataren majalisar dinkin duniya ta bayyana nauyin dake kanta shine taimaka ma sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres don sake fasalin samar da cigaba mai daurewa a duniya.

Amina Mohammed ta lissafa bangarori 11 da majalisar dinkin duniya zata fi baiwa fifiko
Amina Mohammed

Amina ta bayyana haka ne a ganawarta da manema labarai karo na farko da tayi a shelkwatar majalisar dinkin duniya dake birnin New York, kasar Amurka, inda tace samar da cigaba mai daurewa ne kadai hanyar tabbatar da zaman lafiya a duniya gaba daya.

“Babban sakataren majalisar dinkin duniya a shirye yake don samar da canje canje ga yadda ake tafiyar da majalisar, tuni ya bayyana manufarsa da kudirorin dayake dasu game da majalisar. Sakataren ya nanata niyyarsa na magance musabbabin tashen tashen hankula da rikice rikice.

“A shirye yake ya sauya yadda majalisar zata samar da cigaba mai daurewa, sa’annan zai karfafa majalisar ta fannoni daban daban domin samun daman gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata.”

KU KARANTA: Antonio Guterres ya Amina Mohammed a matsayin mataimakiyar sakataran majalisar dinkin duniya

Amina ta bayyana ginshikai guda uku a matsayin wasu hanyoyin da zasu taimaka ma majalisar, ginshikan sun hada da shawo kan matsalar rashin aminci da yarda, karfafa shugabanci da kuma sanya ido kan tabbatar da sakamako mai kyau.

“Zamu kara kaimi akan tsarin mulki, zamu samar da hanyoyin da zasu janyo hankalun mambobin majalisar tare da tabbatar da tsarin majalisar na duba yiwuwar shawo kan matsalolin kasashen.”

Sai dai Amina tace idan dai ana bukatar cin ma burikan da aka sanya a gaba, hakan na bukatar gina tubali mai karko

“Dole ne mu cike gibin dake tsakanin tallafa ma gajiyayyu, samar da cigaba da kuma zaman lafiya a karkashin kare hakkin dan Adam, tare da tabbatar mun baiwa kowa daman shigowa a dama da shi. Haka zalika dole ne mu sake fasalin tsantsanin kudade, da yadda ake tara su. sa’annan sai mun samar da wata lada ga duk wadanda suka hada kai damu don cin ma muradun mu.

“Bugu da kari muna bukatar samar da hanyoyin kulawa da matsalolin da ka iya tasowa da canjin da zamu kawo musamamn a fannin samar da zaman lafiya, cigaba mai daurewa da kuma inganta yanayin muhallin duniya gabaki daya. haka zalika dole nu mu cigaba da wasu tsare tsaren da muka tarar, tare da canza wasu da ba zasu kai mu ga gaci ba.

“Zamu yi hakan ne saboda mafitar da aka samu a baya, ba lallai ne su shawo kan wasu matsalolin da zamu fuskanta a nna gaba ba su kadai.” Inji Amina

Har wa yau Amina ta bayyana shugabanci na gari ba tare da nuna son kai bane kadai zai tabbatar ma majlisar dinkin duniya matsayinta na uwa mai kwaba a duniya, sa’annan haka ne kadai zai tabbatar da hadin kan kasashen duniya tare da samun goyon baya musamman wajen yin tsare tsare, magance matsaloli, sanya idanu da kuma samun sakamako mai kyau.

Daga karshe Amina tace ya zama wajibi su magance matsalar rashin aminci da yarda dake tsakanin kasashen duniya, tace hakan zai samu ne ta gudanar da mulki da gaskiya a kowane matsayi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel