Karin aure: Abin da ya sa muke kokarin kawo gyara-Sarkin Kano

Karin aure: Abin da ya sa muke kokarin kawo gyara-Sarkin Kano

– Mai girma Sarki Sanusi II ya bayyana dalilin da ya sa aka kawo dokar hana aure

– Sarkin Kano yace za a hana talaka yawan aure a kasar sa

– Sau da yawa dai uba bai iya kula da ‘ya ‘yan sa

Karin aure: Abin da ya sa muke kokarin kawo gyara-Sarkin Kano
Karin aure: Abin da ya sa muke kokarin kawo gyara-Sarkin Kano

Mai girma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyana dalilin da ya sa aka kawo dokar nan da ke nema ta hana talaka auren matan da ba zai iya daukar nauyin su ba. Sarki Sanusi II dai yace za a hana talaka tubus kara auren mata a kasar sa.

Sarki Sanusi II ya bayyana yadda ya rika samun koke-koke daga mata game da yadda tsofaffin mazajen su ke watsi da kula da ‘ya ‘yan da suka haifa bayan sun rabu. Sarki yace an taba kawo masa karar wani mutumi mai ‘ya ‘ya 10 da ya gaza kula da su, ko da aka bincika sai aka ga ashe yana da wasu ‘ya ‘ya 8 kuma a wajen wata matar. Wannan mutumi dai ya fadawa mai martaba cewa gyaran takalmi yake yi.

KU KARANTA: Izala ta soki Sanusi II

Sarkin Kano Sanusi II ya bayyana wannan ne a wajen bikin aurar da zaurawa da aka yi a wancan makon. Sarkin yace duk mara arziki bai dace yayi ta aure ba. Sarki Sanusi II ya kara bayyana yadda wannan doka za ta kasance.

Babban malamin Duniya mai fatawa Sheikh Ismail Menk ya goyi bayan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a game da maganar. Sai dai a nan gida wasu Malaman suna ganin cewa da sake.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel