Ina saka kayayyakin da ake yi a Aba - Chris Ngige

Ina saka kayayyakin da ake yi a Aba - Chris Ngige

Ministan kwadago da samar da aikin yi, Chris Ngige ya ce shi ma'abocin sa kayayyakin da ake yi a Aba ne kuma duk kayan da ya ke sawa na cikin gida ne.

Don karfafa sayen kayayyakin da ake samarwa a Najeriya, gwamnatin ta bada damar duba dokar da ta kafa hukumar kula da fataucin kayayyaki, dokar za ta tilasta sayen kayayyakin da ake samarwa a Najeriya

Ina saka kayayyakin da ake yi a Aba - Chris Ngige
Ina saka kayayyakin da ake yi a Aba - Chris Ngige

Ministan kwadago da samar da aikin yi, Chris Ngige ya ce shi ma'abocin sa kayayyakin da ake yi a Aba ne kuma duk kayan da ya ke sawa na cikin gida ne.

Ministan ya bayyana haka ne a Umuahia ranar Litinin 27 ga watan Fabrairu a wajen taron musayar ra`ayi na gwamnatin tarayya, da kuma kaddamar da shirin wayar da kan al`umma mai taken "Canji ya fara daga ni" a jihar Abia.

Ngige ya ce, a da, ya na sayo tufafinsa daga Malaysia kafin daga bisani ya gane wadannan kayan duk ana yin su a gida, musamman ma Aba kuma su na da inganci sosai.

Ministan ya ce, " 'yan Najeriya na da albarkatu da za su ciyar da kasarsu gaba amma dole mu mayar da hankali wajen inganta kayayyakin da mu ke yi."

Ya kuma ce, jihar Abia kamar wasu jihohin Najeriya, na da cikakkiyar damar zama cibiyar masana`antu ta wannan kasa.

Kuma gwamnati mai ci ta zabi Abia a daya daga cikin guraren da za ta kafa masana`antu.

Ngige ya yi kira ga jama`ar jihar su yi amfani da wannan dama wajen kawo canji a jihar don samar da ayyukan yi ga matasan jihar.

Mai masaukin bakin taron kuma ministan yada labarai da al`adu' Alhaji Lai Mohammed ya ce, daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci ga kudurin gwamnatin tarayya na fadada harkokin tattalin arziki shi ne bunkasa kayayyakin da ake a cikin gida.

"Bisa haka ne, zan iya bugar kirji na ce Abia ta ciri tuta".

"A yau jihar ce ke samar da takalman soji masu inganci ga sojojinmu, kuma wannan daya ne daga cikin ababan burgewa da jihar ke samarwa".

"Saboda haka yayin da jihar ke bunkasa samar da kayayyaki a cikin gida, ita kuwa hukumar soji na taimakawa wajen sayen kayayyakin."

Ministan ya ce, don karfafa sayen kayayyakin da ake samarwa a Najeriya, gwamnatin ta bada damar duba dokar da ta kafa hukumar kula da fataucin kayayyaki.

Ya ce dokar za ta tilasta sayen kayayyakin da ake samarwa a Najeriya.

Ga hoton bidiyo na ra'ayin jama'a kan shugaba Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel