‘Galibin yan shi’a na goyon bayan shugaba Buhari’ – inji kungiyar Rasullulah Ahazam

‘Galibin yan shi’a na goyon bayan shugaba Buhari’ – inji kungiyar Rasullulah Ahazam

Wata kungiyar yan shi’a dake jihar Gombe mai suna ‘Ahalul Baytul Muslim committee’ wanda wani sash ice daga bangaren wani darikan shi’a ‘Rasullulah Ahazam’ ta barranta daga mubaya’a ga shugaban kungiyar shi’a ta IMN wato El-Zakzaky, sa’annan ta shirya gangamin addu’ar samun sauki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

‘Galibin yan shi’a na goyon bayan shugaba Buhari’ – inji kungiyar Rasullulah Ahazam
‘Galibin yan shi’a na goyon bayan shugaba Buhari’ – inji kungiyar Rasullulah Ahazam

Kaakakin kungiyar, Malam Badamasi Adamu Ali ne ya bayyana haka, inda yace kungiyar tasu ta damu matuka da rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, don haka ne ma ta shirya yi masa addu’o’in samun lafiya.

KU KARANTA: An gurfanar da malaman addinin kirista gaban kotu kan furta kalaman ɓatanci ga musulunci

Badamasi ya bayyana haka ne a ranar Litinin 28 ga watan Feburairu yayin da suke gudanar da addu’ar a babban masallacin jihar Gombe, kungiyar ta kara da yi ma kasa Najeriya samun zaman lafiya da karin arziki, sa’annan ya musanta batun da ake yadawa wai yan shi’a basa son gwamnatin Buhari.

Ina tabbatar muku da cewa mu yan shi’ar Rasullulah Ahazam muna goyon bayan gwamnatin shugaba Buhari, saboda mu kam muna da rajista da gwamnati, kuma dokar kasa ta san damu.

Daga karshe Malam Badamasi yace kungiyarsu bata daga cikin yayan kungiyar shi’a wanda El-Zakzaky yake jagoranci, don haka basu da wata matsala da gwamnatin tarayya dangane da cigaba da rike shi da take yi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel