Gwamnati zata samar da takin zamani a Najeriya

Gwamnati zata samar da takin zamani a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani sabon shirin tallafawa manoma da taki wanda zai kai ga samar da taki ton 4,000 a makon farko dan tallafawa manoman.

Gwamnati zata samar da takin zamani a Najeriya
Gwamnati zata samar da takin zamani a Najeriya

Shi dai wannan shiri da shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shi a watan Disamba, zai taimaka ne wajen samar da ton miliyan 1 na takin NPK wanda za’a sayarwa manoma akan kudi naira 5,500 sabanin farashin N8,000 da ake sayarwa yanzu haka.

KU KARANTA: Sako daga fadar shugaban kasa

kungiyar manoma ta kasa ta bakin Sakatare kungiyar sakamakon nasarar noman da aka samu, yanzu haka mutane da dama sun rungumi noman rani.

A wani labarin kuma, Duk da cewa darajar Naira bai karu ba idan aka dan ganta da dala a yau Litinin, amma darajar tata ta karu idan aka dan ganta ta da kudin tarayyar turai na 'Euro' da kuma kudin kasar Ingila (Pound) inda yanzu ake saida su a matsayin N480 da kuma N565.

A A ranar Litinin din da ta gabata dai ne CBN ya sanar da cewa ya fitar da wadansu sababbin manufofin musayar kudaden waje.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel