Jihar Nijar ta fara adu’oi na sati daya domin shugaba Buhari

Jihar Nijar ta fara adu’oi na sati daya domin shugaba Buhari

- Mutanen jihar Nijar sun fara addu’a da azumi na mako daya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Kwamishinan labarai, al'adu da yawon shakatawa, Mista Jonathan Tsado Vatsa ya sanar da labari, ya ce za a kawo karshen add’o’in ne 5 ga watan Maris

Jihar Nijar ta fara adu’oi na sati daya domin shugaba Buhari
Jihar Nijar ta fara adu’oi na sati daya domin shugaba Buhari

Gwamnatin Jihar nijar ta bayyana za ta fara addu'o’i da azumi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari na mako daya, wanda ya kasance a kan hutun ganin likita a kasar birtaniya da fatan Allah ya basa lafiya da kuma nasarara gwamnatinsa.

Kwamishinan labarai, al'adu da yawon shakatawa, Mista Jonathan Tsado Vatsa ya bayyana a cikin wata sanarwa ga 'yan jarida cewa, ko da yake alamu na nuna cewa shugaban kasa na cikin koshin lafiya a hutunsa na ganin likita amma akwai bukatar yi masa addu'a domin matsayinsa na shugaban al'umma.

KU KARANTA KUMA: Buhari mutum mai gaskiya da kishin kasa – Inji Shagari

Vatsa ya bukaci dukan mutanen Jihar Nijar da su yi addu'a da azumi musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A matsayin mu na gwamnati muna addu'a kuma mun bukaci duk ‘yan Nijar gaba daya kiristoci da musulmai da su yi wa shugaban kasa addu’a na sati daya wadda za a kawo karshe 5 ga watan Maris 2017.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel