Buhari mutum mai gaskiya da kishin kasa – Inji Shagari

Buhari mutum mai gaskiya da kishin kasa – Inji Shagari

Tsohon Shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari ya yabi Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda ya ke kokarin ganin ya gyara kasar Najeriya.

Buhari mutum mai gaskiya da kishin kasa – Inji Shagari

Shagari ya ce Buhari mutum ne mai gaskiya, rikon amana da kishin kasa.

Yace kokarin da Buhari yakeyi musamman wajen yaki da cin hanci da rashawa sannan da seta Najeriya akan tafarkin kwarai abu ne wanda ya cancanci yabo.

Shagari ya kara da cewa dole a jinjina ma Buhari akan yadda ya ke ta kokarin ganin ya farfado da tattalin arzikin kasa Najeriya da irin shirye shirye da gwamnatinsa ta bullo dasu domin samun nasara akan hakan.

KU KARANTA KUMA: EFCC na neman wata mata ruwa a jallo kan laifin damfara

Shagari ya fadi hakanne a yayin da yake jawabin murnan zagayowar ranar haihuwarsa a garin Sokoto.

Tsohon shugaban kasa Shehu Shagari ya cika shekara 92 a duniya a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana kasan Ingila inda ya ke hutu da duba lafiyarsa.

Ya kira sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman jiya domin mika ta’aziyyar sa ga sarkin a dalilin rasuwar mahaifiyarsa Hajiya Aminatu Mai Babban daki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel