Lauyan Zakzaky ya kai kuka ga Osinbajo

Lauyan Zakzaky ya kai kuka ga Osinbajo

– Lauyan shugaban kungiyar IMN Ibrahim Az-Zakzaky, Femi Falana ya rubuta takarda ga Osinbajo

– Lauyan ya nemi a saki shugaban kungiyar shi’a da ke garkame

– Ana dai cigaba da daure Ibrahim El-Zakzaky bayan tsawon lokaci

Lauyan Zakzaky ya kai kuka ga Osinbajo
Lauyan Zakzaky ya kai kuka ga Osinbajo

Femi Falana SAN Lauyan shugaban kungiyar IMN Ibrahim Az-Zakzaky, ya rubuta wasika ga Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo SAN da kuma Ministan shari’a na kasar Abubakar Malami SAN game da cigaba da daure malamin.

Falana yace idan har gwamnati ba ta saki Zakzaky ba zai dauki mataki. Babban Lauyan yace zai nemi Kotu tayi watsi da karar gwamnatin tarayya da ke babban kotun kasar da ke Abuja idan har ba a saki shugaban Kungiyar na Shi’a ba.

KU KARANTA: Za a daure wasu Fastoci bayan sun zagi musuluci?

A watan Disamban bara Alkali Gabriel Kolawole ya nemi a saki Ibrahim Zakzaky da matar sa ba tare da bata lokaci ba. Alkali mai shari’ar ya kuma nemi a biya su kudi Naira Miliyan 50 sannan kuma a gina masa wani gida cikin Garin Kaduna ko duk inda su ke so bayan barnar da aka yi masu.

Falana yace har yau ba ayi wannan ba kuma ana cigaba da rike Zakzaky. Babban Lauyan yace dole a gaggauta sakin malamin ba tare da bata lokaci ba.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel