GWARZO: Sanata Kwankwaso ya samu lambar yabo a kasar Afrika ta kudu

GWARZO: Sanata Kwankwaso ya samu lambar yabo a kasar Afrika ta kudu

Mujallar African Leadership Margazine (ALM) dake birnin Landan ta baiwa sanata Rabi'u Musa Kwankwaso lambar yabo na gwarzon shekara.

GWARZO: Sanata Kwankwazo ya samu lambar yabo a kasar Afrika ta kudu
GWARZO: Sanata Kwankwazo ya samu lambar yabo a kasar Afrika ta kudu

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya samu wannan lambar yabon ne bisa ga gudummawar da ya bayar a fannonin ilmi da ci gaban al'umma a lokacin da yake gwamna a tsakanin shekara 2011 zuwa 2015, kamar yadda shugaban kwamitin amintattu na mujallar, Ambasada Joe Beasley ya bayyana.

An gudanar da taron ne a Johannesburg babban birnin Afrika ta Kudu.

KA KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya zata samar da guraben ayyuka 350,000 ga matasa

Wasu daga cikin wadanda aka baiwa lambar yabon a baya sun hada da tsohon shugaban kasar Ghana, John Mahama; uwargidan shugaban kasar Afrika ta Kudu, Bongi Ngema-Zuma; matashin biloniyan nan na kasar Tanzania , Mohammed Dewyi da sauransu.

Sai kuma Dakta Mo Ibrahim, shugaba Ellen Johnson-Sirleaf ta kasar Liberia da shugaba Jakada Kikwete na kasar Tanzania.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel