An kashe wani matashin soja lokacin harin Boko Haram

An kashe wani matashin soja lokacin harin Boko Haram

An kashe wani soja mai suna Lance Corporal Chidi Ukelere bayan yaki da yan ta’addan Boko Haram a ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairu na shekaran 2017. Sojan ya kasance daya daga cikin jaruman da yan Boko Haram suka kai ma hari a garin Gajiram, kimanin kilomita 80 daga hanyar Maiduguri, babban birnin jihar Borno, a yammacin ranar Laraba.

A cewar rahotanni, arangaman ya dauki tsawon sa’o’i biyu yayinda aka kashe wasu sojoji sannan kuma wasu suka ji rauni.

KU KARANTA KUMA: Kalli abunda ya faru da wani mutumi shekaru 8 bayan ya musulunta (HOTO)

Wani mai amfani da shafin Facebook, Prince ID Peter ya yada hotunan jarumin da harin ya cika da shi tare da korafin cewa Yan Boko Haram na ci gaba da kai hari duk da ikirarin da gwamnati keyi na cewa ta shafe yan ta’addan baki daya.

An kashe wani matashin soja lokacin harin Boko Haram
An kashe wani matashin soja lokacin harin Boko Haram
An kashe wani matashin soja lokacin harin Boko Haram
An kashe wani matashin soja lokacin harin Boko Haram
An kashe wani matashin soja lokacin harin Boko Haram
An kashe wani matashin soja lokacin harin Boko Haram

Asali: Legit.ng

Online view pixel