Kalli abunda ya faru da wani mutumi shekaru 8 bayan ya musulunta (HOTO)

Kalli abunda ya faru da wani mutumi shekaru 8 bayan ya musulunta (HOTO)

Shekaru 8 bayan ya musulunta, Mahershala Ali ya zamo dan wasa musulmi na farko da yayi nasarar karban lambar yabo mafi girma a duniya kan harkan fina-finai.

Matashin mai shekaru 43 yayi nasarar lashe lambar yabon ne sakamakon rawar gani da ya taka a gurin taron ban girma kashi na 89 a 2017, wanda aka gudanar a jiya, 26 ga watan Fabrairu, a Dolby Thatre a Hollywood dake Los Angeles.

Kalli abunda ya faru da wani mutumi shekaru 8 bayan ya musulunta (HOTO)

Ali ya musulunta a shekarar 1999 kuma kwanan nan ya kwatatanta banbamci da yake fuskanta a matsayinsa na musulmi da kuma banbamcin launin fata a matsayinsa na bakin fata dake zaune a kasar Amurka.

KU KARANTA KUMA: An kama matar dake wadata yan ta’adda da bindiga (HOTO)

An sanya masa sunan wani annabin coci sannan kuma ya taso a gaban mahaifiyarsa, Willicia, wacce ta kasance minister a coci, babu wanda ya san cewa Ali zai canja addini. Ya musulunta kan tafarkin Ahmadiyya, ya canja sunan mahaifinsa daga Gilmore zuwa Ali, sannan kuma ya bi sahun al’umman Ahmadiyya.

Kalli abunda ya faru da wani mutumi shekaru 8 bayan ya musulunta (HOTO)
Mahershala Ali da matar sa

Ali na auran Amatus Sami-Karim. Sun haifi ‘yar sun a fari mai suna Bari Najma a ranar 22 ga watan Fabrairu shekarar 2017.

Muna taya dan wasa Musulmi murna!

Ku biyo mu: https://www.facebook.com/naijcomhausa/ da nan https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel