Kwanaki 38 a kan mulki: abubuwa 7 da Osinbajo yayi a matsayin mukaddashin shugaban kasa (Na 1 da 6 zai sa ka so shi)

Kwanaki 38 a kan mulki: abubuwa 7 da Osinbajo yayi a matsayin mukaddashin shugaban kasa (Na 1 da 6 zai sa ka so shi)

Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin mukaddashin shugaban kasar Najeriya ya cimma nasaran samun wasu shahara mai kyau a tsakanin mutanen Najeriya. Da daman a ganin cewa halin da kasa ke ciki baiyi muni ba, kadan din da Osinbajo keyi yan Najeriya da dama na kallonsa a matsayin mai yawa.

Kwanaki 38 a kan mulki: abubuwa 7 da Osinbajo yayi a matsayin mukaddashin shugaban kasa (Na 1 da 6 zai sa ka so shi)

Har ta kai wasu na fadin cewa sun fi son shi a matsayin shugaban kasa fiye da shugaba Buhari wanda ya bar kasar tun ranar Alhamis, 19 ga watan Janairu, 2017. Ga wasu daga cikin abub uwan da mukaddashin shugaban kasa yayi:

1. Shirin Abinci

A ranar 27 ga watan Janairu, 2017 mukaddashin shugaban kasar ya gudanar da wani ganawa tare da daraktan kungiyar World Food Programme (WFP), Ms Ertharin Cousin.

Kuma a ranar Juma’a, 24 ga watan Janairu, ya yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya na shirye-shiryen gaggawa don kawo sauki ga manoma masu kiwon kaji a kasar domin kare ma’aikatar daga durkushewa.

Ya kuma jagoranci taron yan majalisa a ranar 1 ga watan Fabrairu, inda a nan ne aka bukaci kwamitin gwamnati da su rage farashin kayayyakin abinci a kasar.

2. Alkalin alkalai Onnoghen

Mukaddashin shugaban kasar, a ranar 7 ga watan Fabrairu ya aika da sunan mukaddashin alkalin alkalai na Najeriya, Justis Walter Onnoghen, ga majalisar dattawa domin a tabbatar da shi.

Majalisar dattawa bata riga ta tabbatar da Onnoghen ba tukuna.

3. Kwangilar hanya

A ranar 8 ga watan Fabrairu, ya shugabanci taron majalisa ya kuma bayar da naira biliyan 21 don gina hanyar Ilorin-Omu Aran Kabba, sashi I.

Har ila yau, a ranar 15 ga watan Fabrairu, ya amince da bayar da naira miliyan 126 don aikin hanyar a fadin jihohin Kano, Bauchi, Adamawa, Kwara, Gombe da Kaduna.

4. Ziyartan Niger Delta

A tsakanin 10 da 13 ga watan Fabrairu, Osinbajo ya ziyarci Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa a kokarin ci gaba da tattaunawarsa tare da al’umman yankin samar da mai a yankin Niger Delta.

Sannan ya tafi Port Harcourt, jihar Rivers, don ganawa da masu ruwa da tsaki na garuruwan samar da mai. A lokacin ganawar, ya gudanar da aiki na tsaftace Ogoni Land.

5. CBN da Forex

A ranar 16 ga watan Fabrairu, ya shugabanci taron kungiyar tattalin arziki na kasa na shekarar ya kuma umurci CBN da ta duba manufar canjin kudaden waje.

6. Ziyartan filin jirgin sama na Lagas

Ya kai ziyarar bazata filin jirgin sama na Murtala Muhammed International Airport, dake jihar Lagas a matsayin wani sashi na jirin gyara sana’a cikin kwanaki 60 a kasar.

Ziyaran ya sa da dama daga cikin ma’aikatan filin jirgin cikin mamaki. Osinbajo ya duba hukumomi sannan ya zanta da jami’an filin jirgin.

Kasa da sa’o’I 24 da kai ziyarar bazatan, gwamnatin tarayya ta sanar da koran manyan daraktocin hukumar jirgin sama 10.

Sannan kuma aka nada sababbin daraktoci da Janar manaja a hukumar filin jirgin saman Najeriya (FAAN).

7. Wadata kayyakin aiki

Taron majalisa da Osinbajo ya jagoranta a ranar 22 ga watan Fabrairu, ya amince da bayar da naira biliyan 32 don kammala aikin hanyar Kaduna ta Kudu mai kilomita 50

Kungiyar ta kuma bayar da dala 39.9 don gina gadar da ta sada Kamaru-Najeriya a Ikot Efiem.

A kasa bidiyon yan Najeriya ne dake magana kan halin da kasa ke ciki:

Asali: Legit.ng

Online view pixel