Duk da suka, sarkin Kano ya ci gaba da dokar hana maza matalauta daga auren mata biyu

Duk da suka, sarkin Kano ya ci gaba da dokar hana maza matalauta daga auren mata biyu

- Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi II ya ce ba zai ja da bay aba gurin sanya dokar hana matalauta maza daga auren sama da mata daya

- Sarkin ya kuma yi gargadin cewa za’a hukunta maza masu dukan matansu da kuma masu yiwa ‘ya’yansu mata auran dole

Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi II ya ce duk da sukar da ya samu, ba zai ja da baya ba gurin sanya dokar hana maza masu fama da talauci auren sama da mace daya ba.

Ya yi wannan jawabin ne a jiya, 26 ga watan Fabrairu a lokacin wani auren ma’aurata 1,520 da gwamnatin jihar Kano tayi, yayi gargadin cewa duk da cewan ba wai an sanya dokar don a hana musulmai daga auren mata hudu bane, amma zai ta’allaka ne aka yadda namiji zai kula da matayensa da kuma ‘ya’yansa daidai da koyarwar addinin Islama, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Duk da suka, sarkin Kano ya ci gaba da dokar hana maza matalauta daga auren mata biyu

Yace: “Zamu zauna a ranar Laraban nan mai zuwa domin duba sama da shafuka 80 na doka sannan kuma mu gyara inda ke bukatar gyara kafin mu gabatar da shi ga majalisar dokoki na jihar domin sanya shi cikin doka.

KU KARANTA KUMA: Ana fadin karerayi akan rikicin kudancin Kaduna – ‘Yan sanda

“Mutanen mu na fuskantar babban kalubale a harkokin iyalinsu. Munji korafi da dama inda uba keyi ma ‘yar sa auren dole ba wai da son rant aba. Munji korafi da dama inda mutane ke kara aure alhalin bazasu iya ciyar dasu da kyau ba, basa tufatar da su da sutura mai kyau duk da cewan suna da halin yin haka.

“A wannan al’amari, dokar da za’a gabatar zai magance haka, kotu zata dauki wani abu daga cikin dukiyar mutum domin ta ciyar da iyalinsa sannan ta tufatar da su. Idan mutun ya yi yunkurin take umurnin kotu, toh doka zata yanke mai hukuncin da ya dace da shi. Idan ka san cewa albashin ka bazai iya rike mata sama da day aba toh karda ka kara aure.”

Sanusi ya kuma gargadi musulmai musamman wadanda ke da halin yiwa ‘ya’yansu mata auren dole ko kuma dukan matayensu, da su daina haka, kamar yadda a cewar sa dokar ba zai bari irin wannan abu ya ci gaba ba a jihar.

Ku biyo mu: https://www.facebook.com/naijcomhausa/ da nan https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel