Sanatan jihar Yobe ya gina katafaren Asibiti, ya miƙa shi gudunmuwa ga gwamnatin tarayya

Sanatan jihar Yobe ya gina katafaren Asibiti, ya miƙa shi gudunmuwa ga gwamnatin tarayya

A ranar Asabar 25 ga watan Feburairu ne shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki ya kaddamar da wani sabon katafaren Asibiti mai cin gado 80 wanda sanata mai wakiltar al’ummar Yobe ta kudu Sanata Muhammed Hassan ya gina a garin Potiskum.

Sanatan jihar Yobe ya gina katafaren Asibiti, ya miƙa shi gudunmuwa ga gwamnatin tarayya

Sanata Hassan yace “dalilin daya sanya ni gina wannan asibitin shine sakamakon wani hadarin mota da nayi yayin da nake yakin neman zabe a shekarar 2015, inda wani amini nay a rasu, ni kuma na karya kasusuwan kirji na. hakan ne ya bude mini ido kan gaskiyar halin da asibitocin mu suke ciki.

KU KARANTA: Gwamna Mimiko ya miƙa ma Akeredolu ragamar mulki salin, alin

“Cikin ikon Allah,a yau na kammala gina wannan katafaren asibiti mai cin gadoji 80 a garin Potiskum, kuma na sanya gadoji, magunguna, na’urorin gwaje gwaje da sauran kayayyakin aiki.”

Sanatan jihar Yobe ya gina katafaren Asibiti, ya miƙa shi gudunmuwa ga gwamnatin tarayya

Yayin dayake jawabi, Sanata Saraki ya bukaci gwamnatin tarayya, na jiha dana kananan hukuma dasu tabbatar da ingancin asibitocin kasar nan don amfanin talakawa. Saraki ya kara da cewa samuwar asibitin zai rage ma jama’an yankin wahalhalun yin tafiya mai nisa kafin su isa ga wani asibiti.

“Ina rokon ma’aikatan lafiya data tabbata asibitin nan yana sanin kulawa yadda ya kamata, ina sa ran a gudanar da asibitin nan da kwarewa da sanin ya kamata, kuma jama’an Potiskum ina shawartar daku ribaci amfanin asibitin.” Inji Saraki

Sanatan jihar Yobe ya gina katafaren Asibiti, ya miƙa shi gudunmuwa ga gwamnatin tarayya

Sanatan jihar Yobe ya gina katafaren Asibiti, ya miƙa shi gudunmuwa ga gwamnatin tarayya

Sanata Saraki ne ya fara amfani da kayan aikin asibitin a lokacin daya auna hawan jinin sanata Dino Melaye, taron ya samu halartan manyan mutane ciki har da dattijo Alhaji Adamu Ciroma

Sanatan jihar Yobe ya gina katafaren Asibiti, ya miƙa shi gudunmuwa ga gwamnatin tarayya

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel