YANZU-YANZU: Shugaba Buhari ya kira sarkin Katsina a waya bisa wannan dalili (Karanta)

YANZU-YANZU: Shugaba Buhari ya kira sarkin Katsina a waya bisa wannan dalili (Karanta)

-Shugaba Muhammadu Buhari na waje amma alamu na nuna cewa hankalinsa na gida

-Shugaban ya kira sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Usman a waya a yau Lahadi 26 ga watan Fabarairu.

-Buhari ya yi masa ta'aziyar rasuwar mahaifiyarsa Hajiya Aminatu mai Babban daki ne wacce ta rasu ranar a Asabar

YANZU-YANZU: Shugaba Buhari ya kira sarkin Katsina a waya bisa wannan dalili (Karanta)
YANZU-YANZU: Shugaba Buhari ya kira sarkin Katsina a waya bisa wannan dalili (Karanta)

Shugaba Muhammadu Buhari ya kira Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Usman a yau Lahadi 25 ga watan Fabarairu shekarar 2017 a waya daga birnin Landan.

Shugaban ya kira sarkin ne domin yi masa ta'aziyyar mahaifiyarsa wacce ta rasu a ranar Asabar 25 ga watan Fabarairu a cewar, kakakin shugaban Femi Adesina.

A hirar ta su ta wayar tarho, shugaba Buhari ya yiwa marigayiya Amina addu'ar Allah Ya jikanta, Ya kuma ba sarkin hakurin jure wannan babban rashi.

Shugaba Buhari ya kuma ce, rashin marigayiyar babbar hasara ce ba kawai gare shi kadai ba, har da sauran al'umma baki daya.

Marigayiya Hajiya Aminatu ta rasu ta bar 'ya 'ya 9 ciki har da mai martaba sarki, an kuma binne ta kamar yadda adinin musulunci ya tanada a garin Katsina.

Wannan kira na shugaba Buhari ya zo ne kwana guda bayan da shugaban ya kira masu yi masa hidima a ta fuskar mu'amilla da 'yan jaridu, daya bayan daya ciki har da Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed

Femi Adesina Kakakin shugaban ya ce, shugaba Buhari ya kira shi a waya, ya kuma gode masa kan yadda ya ke fama da 'yan gaza gani kan zaman karbar maganin da ya ke yi a Landan.

Shugaban dai ya kasance a birnin Landan tun ranar 19 ga watan Janairu inda ake duba lafiyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel