YABON GONI YA ZAMA DOLE: Tsohon shugaban kasa ya jinjinawa Shehu Shagari

YABON GONI YA ZAMA DOLE: Tsohon shugaban kasa ya jinjinawa Shehu Shagari

- Tsohon shugaban kasa Jonathan ya taya Shehu Shagari murnar cika shekaru 92 da haifuwa.

- Jonathan ya jinjinawa tsohon shugaban kasa Alh. Shehu Shagari a matsayin dattijo mai adalci da hadin kan ‘yan Najeriya.

YABON GONI YA ZAMA DOLE: Tsohon shugaban kasa ya jinjinawa Shehu Shagari
YABON GONI YA ZAMA DOLE: Tsohon shugaban kasa ya jinjinawa Shehu Shagari

Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya taya tsohon zababan shugaban kasar Najeriya ta farko, Alhaji Shehu Shagari murna, wanda ya cika shekaru 92 da haifuwa a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.

Jonathan, a cikin wani sakon mai girma da mai ba shi shawara kan kafofin watsa labarai ya sanya hannun, Ikechukwu Eze, a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu a birnin tarayya Abuja, ya bayyana Shagari a matsayin "dattijo mai daraja da kuma mutunci, wanda shugabancinsa ya zama wasiyya ga sauran shugabannin".

KU KARANTA KUMA: Na hannun daman Jonathan ya jinjina wa Osinbajo

Tsohon shugaban kasa ya bayyana cewa, bayan mulkinsa, Shagari ya ci gaba da wahayi zuwa ga sauran shugabanin da al'ummomi 'yan Najeriya ta hanyar kishin kasa da kuma sadaukar da zaman lafiya da hadin kan ‘yanNajeriya.

Ya ce: "Ka bauta wa kasar a matsayin malamin koyarwa, dan majalisa da kuma shugaban kasa.

"Mai girma tsohon shugaban kasa ina rokon Allah ya kara ma lafiya da kuma yawancin rai.''

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel