Dala ta fara sauka a kasuwar bayan fage

Dala ta fara sauka a kasuwar bayan fage

Farashin dala ya fadi sosai a karon farko a kasuwannin bayan fage na NAjeriya, kasa da mako guda bayan da babban bankin kasar CBN, ya bayyana matakin bunkasa samar da ita ga masu nema a bankuna.

Matsalar karancin dala a bankunan Najeriya wanda sakamakon rashin wadatar kudaden kasashen wajen a CBN, ya sa dalar ta yi ta tashin gwauron zabi, a kasuwannin bayan fage na kasar.

Dala ta fara sauka a kasuwar bayan fage
Dala ta fara sauka a kasuwar bayan fage

Wasu na ganin wannan ne dalilin da ya sa kayayyakiin masarufi da na amfanin yau da kullum suke kara hauhauwa, duba da cewa kasar ba ta faye fitar da kaya zuwa wasu kasashe ba.

Kazalika kudaden kasashen wajen da take samu ya ragu sakamakon rage sayen man fetur dinta da Amurka ta yi, da kuma janyewar masu zuba jari.

Wasu rahotannin ma sun ce a makon da ya gabata sai da aka sayar da duk dala daya a kan naira 516.

'Yan kasuwar sun ce in abin ya dore, to farashin zai iya dawowa daidai a bankuna da kasuwar bayan fage.

'Yan kasuwar dai sun ce fatansu shi ne dalar ta yi ta sauka domin a samu saukin rayuwa.

KU KARANTA: Zamuyi anfani da jirage wajen fatattakar tsagerun kudancin Kaduna

Wani masanin tattalin arziki a Najeriyar Abubakar Aliyu, ya ce abin bai zo da mamaki ba, kuma idan har matakin bankin ya dore to lallai za a samu sauki sosai.

"Ko a ranar Juma'a ma dalar ta sake saukowa zuwa naira 390 a kasuwar bayan fage," inji shi.

Ya kara da cewa ana hasashen za ta sauko har zuwa naira 350 kan ko wacce dala daya.

"Saboda haka gara ma duk wanda ya san ya boye dala don idan ta yi tsada ya sayar, to a fito da ita yanzu tun kafin ta zame wa mutane asara," a cewar Mista Aliyu.

A ranar Litinin ne CBN ya sanar da cewa ya fitar da wadansu sababbin manufofin musayar kudaden waje.

CBN ya fitar da sabbin manufofin kudin kasashen waje

A karkashin sabon tsarin, Babban Bankin ya ce zai kara yawan kudaden wajen da ya ke bai wa bankunan kasar da nufin saukakawa 'yan Najeriya masu bukatar zuwa asibiti a wasu kasashen, da masu karatu a wasu kasashen da kuma 'yan kasuwa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel